“Kamar Kowa Kake a Yanzu”: Abba Kabir Ya Fayyace Matsayin Aminu Ado a Kano
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya sake magana kan makomar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.
Gwamna Abba ya ce a yanzu Aminu Ado Bayero darajarsa kamar sauran 'yan jihar ne ba tare da bambanci ba.
Kakakin gwamnan, Sanusi Bature shi ya bayyana haka a jiya Laraba 26 ga watan Yunin 2024 a birin Kano, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bature ya ce hukucin Babbar Kotun jihar ya tabbatar da matakin Majalisar na mayar da Aminu Ado kamar sauran jama'a.
"Matakin Majalisar jihar Kano ya tabbata bayan hukuncin kotu, Aminu Ado yanzu kamar sauran 'yan jihar kano ya ke."
"Bai kamata ya rinka mamaye wuraren gwamnati ba, inda ya ke zaune na laka ne wanda ya tilasta kansa zama a can."
- Sanusi Bature
Bature har ila yau, ya zargi wasu 'yan siyasa da zuga Aminu Ado domin ya ci gaba da fafatwa domin neman sarauta.
Ya bayyana cewa lokacin da aka tube Sanusi II babu wani mataki da ya dauka kan gwamnatin da ta shude.
A wani labarin, kun ji cewa kwamishinan 'yan sanda a jihar kano, Salman Garba ya musanta wata alaka da Aminun Ado Bayero.
Salman yana magana ne bayan zargin cewa suna da alaka ta jini da tsohon sarkin wanda mahaifiyarsa ta fito daga jihar Kwara.
Garba ya ce ya zo Kano ne domin yin aiki tukuru da dakile matsalolinta ba wai kare muradun wasu tsiraru a jihar ba.
Asali: Legit.ng