Home Back

'Yan Bindiga Sun Shiga Har Gida Sun Sace Babban Malamin Addini

legit.ng 2024/7/3

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun yi garkuwa da limamin cocin St. Raymond Catholic Church Damba, da ke Gusau, jihar Zamfara, Rev Fr. Mika Sulaiman.

Ƴan bindigan sun sace malamin addinin ne a ranar Asabar, 22 ga watan Yunin 2024.

'Yan bindiga sun sace fasto a Zamfara
'Yan bindiga sun sace babban fasto a Zamfara Hoto: @PoliceNG Asali: Facebook

Muƙaddashin shugaban ɗarikar Katolika na Sokoto, Very. Rev Fr. Nuhu Iliya a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar ya tabbatar da sace Mika Sulaiman, cewar rahoton tashar Channels tv.

"Cike da baƙin ciki a zukatanmu, muna sanar da jama’a game da sace ɗaya daga cikin limamanmu, Rev. Fr. Mika Sulaiman."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan abin baƙin cikin ya faru ne da sanyin safiyar yau, Asabar, 22 ga watan Yuni, 2024 a gidansa.
"Fr Mika Sulaiman shi ne limamin cocin St. Raymond Catholic Church Damba, da ke Gusau, jihar Zamfara."

- Fr. Nuhu Iliya

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Lokacin da Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kakakin ƴan sandan ya ce an yi garkuwa da Mika Sulaiman ne da misalin ƙarfe 3:00 na daren ranar Asabar a gidansa da ke unguwar Damba a Gusau.

"Eh tabbas lamarin ya auku, amma ba a sanar da ƴan sanda da wuri ba. Yana zaune ne shi kaɗai a gidansa wanda yake a can bayan gari."
"Mun tura jami'an tsaro waɗanda suka bi sahun bayan ƴan bindiga kuma Insha Allah za a kuɓutar da shi."

- ASP Yazid Abubakar

Asali: Legit.ng

People are also reading