Tinubu ya yi ta’zaiyyar rasuwar Kabiru Yusuf
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aike da ta’zaiyyar rasuwar wani gogaggen ɗan jarida, Kabir Yusuf.
Marigayi Yusuf ya rasu a jiya Talata bayan kammala aikin Hajji na bana ya koma Kano a karshen Mako.
Kafin rasuwar sa, marigayin shi ne wakilin jaridar The Triumph da Radio France a Abuja.
A sanarwar da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale a yau Laraba, Tinubu ya taya iyali, ƴan uwa da abokan arziki na mamacin jimamin rasuwar ɗan jaridar.