Home Back

Kaduna: Gwamna Uba Sani Ya Mayar da Basaraken da El-Rufai Ya Tsige Kan Kujerarsa

legit.ng 2024/10/5
  • Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya mayar da Cif Jonathan Zamuna, sarkin Piriga zuwa kujerarsa
  • Tsohon Gwamna El-Rufai ne ya tuɓe basaraken daga karagarsa a shekarar da ta gabat kafin miƙa mulki ga magajinsa
  • Gwamna Sani yace ya zame masa dole ya bi dokar kotu domin hakan ta yanke a kan batun tsige basaraken

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya mayar da nadin Sarkin Piriga, Cif Jonathan Zamuna, wanda tsohon Gwamna Nasiru El-Rufai ya sauke daga kujerarsa.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa dole ne ya yi biyayya ga hukuncin da kotu ta yanke kan tsige basaraken.

Uba Sani ya mayar da sarkin da El-Rufai ya kora. Hoto daga @GovKaduna
Gwamna Sani Ya Mayar Da Basaraken Da El-Rufai Ya Tsige Kan Kujerarsa Asali: Twitter

Gwamna ya mayar da sarki kan mulki

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, gwamnan ya sanar da mayar da basaraken a ranar Alhamis yayin wani taron majalisar sarakunan jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce:

"A matsayin alamar mayar da hankali da nayi wurin bin doka, ina son in sanar da ku cewa zan bi umarnin da kotu ta bayar a ranar 10 ga Yunin 2024.
"Kotun ta bayar da umarnin a mayar da Sarkin Piriga, da ke a ƙaramar hukumar Lere, Mai martaba Jonathan Zamuna kan kujerarsa."

"Shugabanci nagari shi ne jigo" - Uba Sani

Gwamnan jihar na Kaduna ya ce shugabanci nagari ne ke zama babban jigo wajen shawo kan ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta.

Gwamnan ya yi nuni da cewa sarakuna sune mafi kusa da jama'a kuma shugabancin su ne wanda ke da saurin kawo gyara a tsakanin al'ummar, inji rahoton The Nation.

Idan za a tuna, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Gwamna Nasir El-Rufai ya sauke Cif Jonathan Zamuna a ranar 22 ga Mayun 2023, kwanaki kaɗan kafin mika mulki ga Uba Sani.

Sanusi II ya zama sarkin Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta bayyana Malam Muhammadu Sunusi II a matsayin sabon Sarkin Kano bayan da ta rushe masarautun jihar biyar.

Tun bayan shan rantsuwa da Abba Kabir Yusuf ya yi a watan Mayun 2023 ake ta sa ran zai dawo da tsohon sarkin Kanon da Gwamna Abdullahi Ganduje ya tsige.

Asali: Legit.ng

People are also reading