Tinubu Ya Amince da Ba Iyalai 3.6m Tallafin N50,000, an Fayyace Tsarin Shirin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da raba N50,000 ga iyalan Najeriya har miliyan 3.6.
Tallafin zai zo ne karkashin hukumar tallafawa iyalai domin rage musu radadin halin da ake ciki yanzu a kasar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Tinubu a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tallafin zai kunshi akalla iyalai 50,000 zuwa 100,000 daga duka jihohin Najeriya har na tsawon watanni uku.
"Shugaba Tinubu ya amince da raba tallafi ga iyalai a duka shiyyoyi guda shida da ke Najeriya karkashin hukumar tallafawa iyalai."
"Daga cikin abubuwan da ke karkashin shirin akwai siyan motoci masu amfani da gas da bas bas domin inganta al'umma."
"Za a ba da tallafin 50,000 ga iyalai akalla 100,000 a kowace jiha da ke Najeriya har na tsawon watanni uku."
Ajuri Ngelale
Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa da kuma hauhawan frashin kaya.
A wani labarin mai kama da wannan, mun kawo muku cewa Gwamnatin Tarayya ta fitar da sabuwar sanarwa kan ba 'yan Najeriya tallafin N50,000.
Wannan tallafi na daga cikin tsarin shugaban kasa Tinubu na ba da tallafin rage radadi (PCGS) domin kawowa jama'a saukin rayuwa.
Za a bada tallafin ne ga kananan 'yan kasuwa da kuma masu sana'o'i a fadin kasar domin rage radadin halin da ake ciki a yanzu.
Asali: Legit.ng