Home Back

Wata Mata Zainab Ta Soka Wa Mijinta Wuka Har Lahira, Ta Yi Bayanin Abin da Ya Faru

legit.ng 4 days ago
  • Ƴan sanda sun kama wata matar aure Zainab Isa bisa zargin daɓawa mijinta wuta har lahira a Abbari da ke cikin Damaturu a jihar Yobe
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar DSP Dungus Abdulkareem ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da saɓani ya shiga tsakanin ma'auratan
  • A kalamata, Zainat ta ce ba da gangan ta kashe sahibinta ba, akasi aka samu a kokarin kare kanta da wuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Wata matar aure ‘yar shekara 22 ta daba wa mijinta wuka har lahira a unguwar Abbari da ke Damaturu babban birnin jihar Yobe a Arewa maso Gabas.

Matar mai suna Zainab Isa yar kimanin shekara 22 ta hallaka mijinta Ibrahim Yahaya ɗan shekara 25 da wuƙa a lokacin da sa'insa ya haɗa su.

Taswirar jihar Yobe.
Yan sanda sun kama matar da ake zargin ta kashe mijinta a Yobe Asali: Original

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkareem ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Damaturu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tuni ƴan sanda suna kama Zainab kuma rundunar ba ta ji daɗin abin da ya afku ne wanda ya zama ajalin matashin magidancin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, ofishin ‘yan sanda na C ya samu korafi daga wani makwabcinsu da ke unguwar Abbari a Damaturu, cewa ma’auratan sun samu rashin jituwa wanda ya rikide zuwa faɗa.

Ya ce makwabcin ma’auratan ya shaida wa ‘yan sanda cewa matar ta yi amfani da wuka ta daba wa mijin a kirji wanda hakan ya zama ajalinsa kafin ƴan sanda su kariso.

Kakakin ‘yan sandan ya ce sun miƙa Zainab zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar (CID) domin gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da ita a gaban kotu.

Yayin da take amsa laifin a hannun ƴan sanda, matar ta ce ba ta yi niyyar kashe mijinta ba, sai dai ta yi amfani da wuƙa ne domin kare kanta, rahoton Channels tv.

Zainab ta ƙara da cewa babu wani farin ciki a zaman aurnsu, kullum cikin faɗa da tashin hankali suke musamman idan ta nemi abinci ko kuɗi daga majinta.

A wani rahoton Yan bindiga sun kai hari masallaci a lokacin da mutane ke shirin Sallar Asuba a kauyen Tazame da ke ƙaramar hukumar Bungudu a Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun kashe ladani da ƙaninsa, sun yi awon gaba da mutane da dama yau Talata da safe.

Asali: Legit.ng

People are also reading