Home Back

Sauyin Yanayi: Dabarun Da  Za Su Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi

leadership.ng 2024/5/7
Sauyin Yanayi: Dabarun Da  Za Su Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi

Akasarin masu kiwon Kifi, na dogara ne a kan kasancenwar yadda yanayi yake, musamman na samar da tsaftataccen ruwa da kuma yadda yanayi zai kasance na zafi ko sanyi, wanda hakan musamman zai ba su damar sanin samun sauyin yanayi.

Babban abin da ke shafar masu sana’ar  kiwon Kifi shi ne, samun yanayin zafi ko na sanyi da kuma samun sauyi na saukar ruwan sama, wanda ke jawo afkuwar annobar ambaliyar ruwan sama da fari.

Wata illar kuma na afkwa ne a cikin dan kankanin lokaci, misali samun ruwan sama kamar da bakin kwarya, inda kuma wata illar ke afkuwa ta dogon zango, wanda za a rika samun sauyi a hankali a hankali.

1- Wanzar Da Dabarun  Kula Da Kiwon Kifin Yadda Ya Dace:

 A cewar Soto, “Wanzar da dabarun kula da kiwon kifi ne mataki na farko na jure wa sauyin yanayi ne zai inganta wajen kiwon su tare da ba su kariya daga kamuwa da cututtuka, sakamakon sauyin yanayi, duba da yadda garkuwar jikin dabbobi ta take, domin kuwa ba sa son yanayi na takura”.

Duba da yadda yanayin muhalli yake, zai  ba da dama wajen rage fuskantar sauyin yanayi tare da inganta kiwon lafiyarsu, abincinsu da kuma ingancin ruwan shansu.

2- Fashin Baki Kan Abin Da Zai Iya Afkuwa A Wajen Kiwon Su:

Ga wanda zai fara wannan kiwo, ana so ya zabi wajen da ya dace da kuma tsarin da zai yi, don guje wa abin da zai iya afkuwa a bangaren sauyin yanayi mai tsanani.

3- Raba Kafa A Yayin Kiwon: Masu iya magana na cewa, ‘Ba a zuba kwai a cikin kwando daya’, wato ma’ana, ana so ka raba kafa ta hanyar yin wata dabara a kan kayanka, don kaucewa yin asara.

Kazalika, raba kafa na taimakawa wajen kara bunkasa kiwo da kuma kara sama wa mai kiwon kudin shiga.

4- Amfani Da Gargadin Farko: Ana so masu kiwo su rika bibiyar bayanai a kan afkuwar sauyin yanayi, wanda hakan zai ba su damar daukar mataki a kan lokaci, domin su kauce wa yin asara.

5- Amfani Da Ingannatun Kayan Aiki Don Yin Kiwo:

Kwamin kiwonsu da ake ginawa a kasa da kuma wanda ake ginawa a kan tudu, ana so a ba su kariya daga afkuwar ambaliyar ruwa. Kazalika, ana so kwamin ya kasance mai zurfi, domin bayar da kariya daga fari da kuma yanayi mai zafi.

6 Ana So Mai Wannan Kiwo Ya Rika Tuntubar Sauran Masu Kiwo:

Akasarin masu kiwo, ba zai yiwu su tafiyar da komai su kadai ba, saboda haka, ana bukatar su rika tuntubar sauran kungiyoyin da ke kiwon Kifi; don samun shawarwarin da za su taimaka musu.

People are also reading