Home Back

Hankalin Silva ya tafi Barcelona, Arsenal da Man City na son Guimaraes

bbc.com 2024/5/5
 Bernardo Silva

Asalin hoton, Getty Images

Bernardo Silva ya yanke shawarar barin Manchester City, dan wasan na tsakiya na Portugal mai shekara 30, wanda kwantiraginsa ya tanadi sayar da shi a kan fam miliyan 50, ya zaku ya tafi Barcelona. (Sport )

Arsenal da Manchester City na duba yuwuwar sayen dan wasan tsakiya na Newcastle United Bruno Guimaraes, na Brazil mai shekara 26 a bazara. (Telegraph)

Chelsea na neman bayani a kan matashin dan bayan RB Leipzig da Faransa Castello Lukeba, mai shekara 21, wanda yarjejeniyarsa da kungiyar ta Jamus ta tanadi sayar da shi a kan fam miliyan 60 ga duk kungiyar da ke bukatarsa. (FootMercato)

Kociyan Manchester United Erik ten Hag na son ganin kungiyar ta sayo wani mai kai hari a bazara domin karfafa gabanta. (Goal)

Akalla akwai tazarar fam miliyan 13 tsakanin Manchester United da Newcastle United a kokarin da suke yi na cimma yarjejeniyar diyya domin daukar darektan wasanni Dan Ashworth, wanda United ke son dauka daga Newcastle. Kuma tuni Magpies din ta sa ya fara hutu kafin cinikin ya tabbata. (Telegraph)

Dan bayan Chelsea Thiago Silva, mai shekara 39, ya cimma yarjejeniya ta baka da Fluminense, kasancewar dan Brazil din zai kasance babu kwantiragin wata kungiya a tare da shi a karshen kakar nan. (Goal)

Tsohon dan gaban Arsenal da Manchester United Robin van Persie na dab da fara aikinsa na kociya na farko, bayan ya tattauna da kungiyar Heerenveen ta Holland. (Algemeen Dagblad )

Real Madrid ta shirya tsawaita kwantiragin dan bayanta na Sifaniya Lucas Vazquez mai shekara 32, wanda kwantiraginsa na yanzu zai kare a watan Yuni. (AS )

Paris St-Germain ta dage haikan wajen ganin ta sayi matashin dan wasan Barcelona Lamine Yamal dan Sifaniya mai shekara 16. (Le Parisien )

Manchester United na son sayen dan bayan Inter Milan Alessandro Bastoni, mai shekara 25, kuma a shirye take ta biya fam miliyan 52 a kan dan Italiyar. (Fichajes)

Kungiyar Feyenoord ta Holland na sha'awar dan wasan gaba na gefe na Tottenham Bryan Gil, na Sifaniya wanda ake sa ran zai bar Tottenham a bazara. (Standard)

Dan gaban Faransa Olivier Giroud, mai shekara 37, zai kulla yarjejeniya da kungiyar MLS ta Los Angeles kuma zai koma kungiyar ta Amurka ne a matsayin dan wasan da ba shi da kungiya a bazara lokacin da kwantiraginsa da AC Milan zai kare. (RMC Sport)

People are also reading