Home Back

Kikikakar Masarautar Kano Tsakanin Sanusi Da Aminu…

leadership.ng 2024/7/5
masarautar kano

Gurbin sarki ya samu ne a masarautar Kano mai dimbin tarihi yayin da a ranar 6 ga watan Yunin 2014, Allah ya yi wa mai martaba marigayi Alhaji Ado Bayero rasuwa bayan shafe shekaru 51 yana mulki.

Bisa al’ada masu zaben sarki ne za su aike wa da gwamna jerin sunayen wadanda suka bayyana sha’awarsu ko wadanda aka ayyana, shi kuma gwamna ya zabi duk wanda ya gama dama a ciki.

Masu iya magana na cewa; rabon kwado ba ya hawa sama ko ya hau ma zai sauko. Ashe rabon tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Malam Sanusi Lamido Sanusi ne ya zamo Sarkin Kano. Ranar 8 ga watan Yuni ne Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya zabe shi don maye gurbin marigayi Alhaji Ado Bayero, kwana biyu bayan rasuwarsa.

Ko da zamowarsa Sarki wanda dama shi ne babban burinsa na rayuwa, Sanusi Lamido ya fara gudanar da sauye-sauye a wani salon shinfida mulki dan zamani. Farawa da bukatar a kira shi da sunan Muhammadu Sanusi II, da kuma aiwatar da gyaran fadar Kano tare da yi mata ado na zamani mai kayatarwa. Haka tafiya ta tafi har sai da mulkin Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya kare Abdullahi Umar Ganduje ya gaje shi.

Da farko alaka tsakanin shugabannin biyu na tafiya daidai kafin ta koma tafiyar Agwagwa. Dangantakar ta yi tsami ce tun bayan da Sarki Sanusi ya fara sukar wasu daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Umar Ganduje kamar batun ciwo bashin biliyoyin dalar Amurka don gina jirgin kasa mai amfani da wutar lantarki.

Wannan suka dai ba karamin tasiri ta yi ba wajen dagula wa gwamtin Ganduje lissafi kasancewar sarkin ya yi ta ce a birnin Ikko kuma duk kasa baki daya ta gani.

Ba iya gwamnatin jiha kawai sukar Sarki Sanusi ta tsaya ba, hatta gwamnatin tarayya ma ba ta tsira ba, don haka ne makusanta Ganduje suka fara kitsa masa kawai ya yar da kwallon mangwaro ya huta da kuda. Amma Ganduje ya yi taka-tsantsan saboda abin da yake shirin yi zai shiga tarihin da ba za a taba mantawa da shi ba.

Dangantaka ta yi tsami
A kowanne rikici tabbas akwai masu amfana daga cikinsa. A wannan lokacin ‘yan gaba-gaba na jikin gwamna suke kara ruruta wutar rikicin.

Kamar yadda ya fada da bakinsa a yayin wata hira da yayi da a rediyo, suna da masaniyyar cewa sarkin yana goyon bayan jam’iyyar PDP zaben 2015, wanda bai kammala ba kuma har ya je wurin shugaban kasa yana son lallai a bai wa Abba. A cewar Ali Baba a gama lafiya mai bai wa Gwamna Abdullahi Ganduje shawara a fannin addinai.

Haka kuma a ranar wata Sallar Idi, Gwamna Ganduje ya makara amma Sarki Sanusi ya ki saurarawa ya karaso, sai a hanya gwamnan ya samu Sallar.

Daga nan, Gwamna Ganduje ya kudiri aniyar ramawa kura aniyarta, Gwamnatin Ganduje ta shirya wata sabuwar doka a karkasa masarautar Kano zuwa 5. Daga cikin sabbin da za aka kirkiro masu daraja ta daya sun hada da: Masarautar Rano da Gaya da Karaye da kuma Bichi.

A cikin dokar, za a zabi shugaban majalisar Sarakunan Kano duk bayan wani lokaci, amma Sarki Sanusi ne a matsayin na farkon shugaban majalisar, sannan kuma idan shugaban ya gaza halartar zaman majilisar sarakunan ba tare da wani dalili ba har sau uku ba, to gwamna zai iya tsige shi tare da maye gurbinsa da wani.

Masu zuga sun zuga
Duk da shi ma Gwamna Ganduje na neman hanyar da zai rama laifukan da Sarki Sanusi ya yi masa, amma magana daga bakin Ali Baba ta tabbatar da cewa “duk wani wanda yake makusancin Ganduje sai da ya ce a sauke Sarki Sanusi” ko ba komai, Rabiu Musa Kwankwanso da Sarki Sanusi za su dandana. Kenan an jefi tsuntsu biyu da dutse daya.

A ranar 21 Nuwambar 2019 ne gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ya yi buris da umarnin kotu na dakatar da shi daga lissafa sabbin masarautu 5 da ya kirkira a matsayin halstattu, inda ya ci gaba da mu’amalantarsu a sha’anin mulki a matsayin halastattun sarakuna.

Daga karshe dai bayan abu ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin masarautar da Gwamnatin Kano, Gwamna Ganduje ya sauke Sarki Muhammadu Sanusi II daga kan mulki a ranar 9 ga watan Maris 2020. Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa da ma can Sarki Sanusin ba cancanta ba, kawai dai tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ne yake son bakanta wa shugaban kasa Jonathan rai, saboda ya tsige Sanusi Lamidon daga shugabancin gwamnan babban bankin kasa.

Abin murna a gidan Bayero
Bayyana sunan Aminu Ado a matsayin wanda zai zamo Sarkin Kano na 15, ya kasance wani babban abin farin ciki ga ahalin Bayero, domin bayan gadar mahaifin dan’uwansa ma Sarki Nasiru Ado ya zama sarki mai daraja ta daya a masarautar Bichi.

Komai na tafiya daidai har da lokacin zaben 2023, inda tsagin jam’iyyar NNPP suka zargi masarautar Kano da goyon bayan jam’iyyar APC mai mulki, wanda wannan ta sanya suka fara lissafin matukar suka samu damar lashe zaben za su dauki mataki kamar yadda APC ta sauke Muhammadu Sanusi II.

Bayan kurar zabe ta lafa, NNPP ta yi nasara a zabe da kuma kotu, sai Gwmanan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnatinsa ba a waiwayi maganar masarautu ba har kusan shekara guda. Amma akwai kishin-kishin na cewa gwamnan na son cire Sarki Aminu da kuma dawo da Muhammadu Sanusi II.

An yi wa Sarakunan Kano murabus
Kwatsam a ranar 23 ga watan Mayu 2024, sai aka jiyo majalisar dokoki ta Jihar Kano a arewacin NIjeriya ta amince da rushe duka masarautun jihar bayan soke sabuwar dokar da ta kirkiri sababbin masarautu a 2019. Hakan na nufin cewa an koma amfani da tsohuwar dokar da ta kafa masarautar Kano.
Kuma gwamnatin Kano ta sanar da jami’an tsaro da su hana Sarki Aminu Ado shigo wa jihar, domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Sake zama Sarkin dunkulalliyar Kano
Bayan Shekaru 4, kimanin kwanaki 1,545 da Gwamna Ganduje ya sauke shi daga sarautar Kano a 2020, Sarki Muhammadu Sanusi II ya dawo a karo na biyu. Hakan dai ya faru ne sakamakon amincewa kudirin da ‘yan majalisar Kano suka zartar na soke dokar da ta kirkiri masarautar Kano.

A jawabinsa, Sanusi II, ya ce; Sabon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da ‘yan majalisar dokoki kan matakin da suka dauka, inda ya ce tabbas duk abin da Allah SWT ya kaddara, babu wanda ya isa ya hana shi afkuwa tun da tun farko ya tsara abinsa. Sarkin ya bayyana haka ne jim kadan bayan karbar takardar mayar da shi kan kujerar sarauta a gidan gwamnatin Kano.

Sarki biyu a masarauta daya
Duk da tsige shi da kuma hana shi shigowa jihar, Sarki Aminu Ado sai da ya dawo Kano a ranar Asabar 25 ga watan Mayu. Wanda kuma komawar tasa ta dumama lamarin tsaro a jihar, har ta kai ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umurni ga jami’an tsaro su kama sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero saboda zaman dardar a cikin jihar.

Aminu Ado Bayero tare da rakiyar wadansu magoya bayansa ya sauka a filin jirgin saman, Malam Aminu Kano da ke birnin, inda bayanai suka nuna cewa ya koma Kano ne domin ya shiga cikin gidan sarauta bisa la’akari da cewa maganar cire shi na gaban kuliya.

Sai dai gwamnatin Jihar Kano da ta samu bayanai cewa Aminu Ado Bayero zai koma Kano, sai gwamna Abba Kabir Yusuf da wadansu kusoshin gwamnati suka yi maza da misalin karfe daya na dare a ranar Juma’a suka yi wa Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu rakiya zuwa cikin fadar Sarkin Kano.
Bayanai sun nuna cewa Sarki Muhammadu Sanusi da wadansu jami’an gwamnati a cikin fadar sarkin Kano suka kwana.

Sarki Aminu ya amince da Tsige shi daga baya ya ki amincewa?
An hasko Sarki Aminu Ado a wani hoto a filin sauka da tashin jirgin Jihar Ribas lema a sauke, hakan na nufin sarki me ci ne kawai ake sanya wa lema ko ya amince da tsige shi?
A gidan rumfa kuwa wanda nan ne babbar fadar Kano take, an ga wani faifan bidiyo yana yawo a kafafen intanet, wanda yake nuna Sarki Sanusi yana korafin duk an cire kayan alatun gidan wasu kuma an lalata.
Bayan tsige Sarakunan dai, Gwamnan Kano ya ba su awanni 48 su tattara kayansu su fice daga fadarsu tare da mikata ga shugaban kananan hukumomin Kano kuma mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu AbdulSalam, cire kayan fadar ya sanya wasu suke ganin ya amince zai fitan, amma kuma daga bisani komai ya sauya. Domin kuwa Sarki Aminu Ado shi ma ya ayyana kansa a matsayin halastaccen Sarkin Kano har ya gudanar da zaman fada a wata karamar fada da ke unguwar Nassarawa.

Umarnin kotu ya daguwala lissafi
Kotuna da dama sun bayar da umarni tun da aka tsige Sarki Aminu, farko dai Sarkin Dawaki, Aminu Babba ne ya shigar da kara a gaban alkalin kotu mai shari’a Mohammed Liman da ke birnin tarayya Abuja, inda kotun ta bayar da umarnin dakatawa da cire Sarki Aminu da nada Sarki Sunusi har sai ta kammala sauraron karar da ke gabata.

Haka zalika, wata kotun Jihar Kano karkashin mai shari’a, Aisha Adamu Aliyu ta umarci kwamishinan ‘yansandan jihar da ya karbe ragamar mulki tare da fitar da sarki na 15, Aminu Ado Bayero daga fadar gidan Nassarawa da kuma hana Sarakunan Kano da Bichi da Gaya da Rano da Karaye gabatar da kansu a matsayin sarakuna har zuwa lokacin da za a kammala sauraron karar da aka shigar a gaban kotu.

Wata kotun tarayya mai zamanta a Kano ta sake bayar da umarnin a fitar da Sarki Muhammadu Sunusi II daga gidan Rumfa da ke kofar kudu, bayan da Sarki Aminu Ado ya shigar da karar rashin amincewa da cire shi a ranar Talata.

Kafin kai wa ga cire Sarki Sunusi, sai ga wani sabon umar kotun mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta babbar kotun Kano da ke zamanta a kan titin Miller, wacce ta hana ‘yansanda da hukumar tsaro na farin kaya (SSS) da sojojin Nijeriya tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Kwamacala Ta Yi Yawa Alkalin-alkalan Nijeriya Ya Fusata
Garin irin wannan tufka da warwara ce ta sanya Alkalin-alkalan Nijeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola ya aike da sammaci ga manyan alkalan babbar kotun tarayya ta Jihar Kano su gurfana gabansa, sakamakon bayar da umarni masu karo da juna.

Wannan kiranye dai za a iya cewa ya zama dole sakamakon tuni masu sharhi suka fara nuna tsoronsu da lalacewar fannin shari’a a kasa baki daya, har an fara dawowa daga rakiyar alkalai a Nijeriya.
Zuwa lokacin hada wannan rahoton dai ba a samu sakamakon ganawar alkalin alkalan da manyan alkalan biyu ba, sannan kowanne daga cikin sarakan ya ci gaba da zaman fada a inda yake, yayin da su kuma Kanawa wadanda abin bai shafa ba kai-tsaye ke ci gaba da gudanar da harkokinsu.

People are also reading