Home Back

RA’AYIN PREMIUM TIMES: Bai dace a yi gaggawar kinkimo aikin titin Legas zuwa Kalaba ba, a halin da Najeriya ke ciki

premiumtimesng.com 2024/5/19
TSADAR RAYUWA: Jigon APC ya ba Tinubu laƙanin gyara kurakuran da ya tsunduma Ƴan Najeriya cikin tsomomuwa

Yanzu dai kusan a ce an fara aikin ginin danƙareren titin da zai tashi daga bakin ruwan Legas zuwa Kalaba a cikin ruɗu da zargin ba a bi ƙa’idojin da ke tattare da tsarin bayar da kwangiloli ba. Amma kuma gwamnatin Bola Tinubu ta yi ƙememe tare da toshe kunnuwa daga sauraren ƙorafe-ƙorafen jama’a masu ganin an karya doka, kuma bai kamata a kinkimo wannan aiki a lokacin da Najeriya ke fama da ruɗanin rashin tabbas ɗin tattalin arziki.

Za a shafe shekaru takwas ana aikin gina titin mai tsawon kilomita 700, wanda za a kashe Naira tiriliyan 15 da toliya wajen aikin. To tabbas adadin kuɗaɗen da aikin zai lashe sai sun haura haka, musamman ganin yadda tsadar rayuwa a Najeriya ke ƙara yin toroƙo ta na tashi sama.

Wannan aiki zai yiwu ya na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya. To amma fa akwai alamomin tambaya sosai a kan aikin. Musamman ganin yadda manyan kakakin gwamnatin tarayya ke jaddada cewa tattalin arzikin Najeriya ya ranƙwafa, har ma ya yi doron ƙusumbi.

An fara aikin titin daga Eko Atlantic City, inda za a kashe Naira tiriliyan 1.06 zuwa Tashar Jirgin Ruwa ta Lekki, kuma har ma an fitar da adadin kuɗaɗen.

Aikin titi ne mai hannu 10 za a fara, kuma kowane kilomita 1 zai lashe Naira biliyan 4. Kuma zai kasance irin sa na farko a Afrika, kamar yadda Ministan Ayyuka, David Umahi ya bayyana.

Irin yadda Minista Umahi ke azarɓaɓi, karkarwa da gaggawar ganin an fara aikin titin, ya sa da dama ana yi masa wani kallon-kallon wani tunani daban.

Rukunin farko na mutanen da aka fara rushe wa kadarori domin fara aikin, tuni har an biya su Naira biliyan 2.75, kuɗin diyyacikin makon jiya.

Bayan wannan aikin titi na Legas zuwa Kalaba, akwai kuma aikin titin Sokoto zuwa Badagry da na Enugu zuwa Abakaliki-Ogoja-Kamaru, wanda ake ganin idan an yi hakan, to kamar wasu shiyyoyi su ma za su ci gajiyar shirin. Shi wannan ba ƙarshen idan an tashi yin sa, zai keta a Oturkpo a Jihar Benuwai har zuwa Jihar Nasarawa, sannan ya gangara Apo, Abuja FCT.

“Wannan kashi na biyu na aikin titina kuwa mun gama tsara shi. Da zarar Shugaban Ƙasa ya amince, to za a fara shi daga Sokoto.”

Idan aka kalli nisan kilomita 1,000 daga Sokoto zuwa Legas, to aikin sai ya lashe Naira tiriliyan 20.

Tuni kwangilar titin Legas zuwa Kalaba ta haifar da ja-in-ja a siyasance, musamman yin la’akari da cewa ba a bi sharuɗɗan da dokar bayar da kwangiloli ta gindaya ba.

Saboda ba a bi sharaɗin kiran kamfanoni su yi takarar neman kwangilar ba, kamar yadda doka ta tanadar, wato Dokar Kwangiloli ta 2007, Sashe na 16 (1) (1) da (d).

Kuma shi da kan sa Minista Umahi ya ce an jingine tsarin bada damar shiga takarar neman aikin ga kamfanoni. To wannan ya sa ana ta tantamar sahihancin gaskiyar adadin kuɗaɗen da ake cewa za a kashe wajen aikin. Naira tiriliyan 15 dai sun kai adadin kasafin kuɗin jihohin Najeriya 36 baki ɗaya na 2024. Su ne za a kashe a aikin titin Legas zuwa Kalaba, a wannan hali na tsadar rayuwa da ake ciki a Najeriya.

Shin ko dai wasu abokan masu mulki ne aka yi wa alfarma aka ba su kwangilar a ɓoye? Ko kuwa kawai daga yanzu gwamnati ta daina bin ƙa’idojin da ke shimfiɗe a cikin Dokar Bada Kwangiloli ta 2007 ne?

Abin mamaki ne a ce gwamnati ta kinkimo wannan gagarimin aiki, a daidai lokacin da tattalin arzikin ta ke dawurwura da dabur-dabur. Ga titina masu tsawon dubban kilomita lalace a cikin ƙasar nan ba a kammala gyare-gyaren wasu ba, wasu kuma ba a ma ko yi maganar gyaran su ɗin ba. Najeriya ce ta can a 131 cikin ƙasashe 141 na duniya wajen lissafin ƙasashe masu nagartattun titina. Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ɗauko aikin gyaran titina, maimakon gina sabbi. Amma har yanzu ba a kammala aikin da yawa cikin waɗannan titina ba.

Titin Abuja zuwa Lokoja ba a kammala ba, haka titin Abuja zuwa Kaduna da sauran titina masu yawan gaske a faɗin ƙasar nan, a yankunan Kudu da Arewa. A kullum sai haɗurra ake fuskanta kan titinan, saboda rashin gyara.

Waɗannan ayyukan da ba a kammala ba ne gwamnatin Buhari ta tafi ta bar wa wannan gwamnati gadon bashi har na Naira tiriliyan 6. Cikin 2023 an tsakuri Naira biliyan 300 an bayar domin samun sauƙin lamarin, amma ko kartar ƙasa da cebur da diga ba su isa ba.

Yakamata gwamnatin Tinubu ta yi taka-tsantsan wajen kashe kuɗaɗen al’umma. Babu wani dalilin da zai sa a yi ta azarɓaɓin fara aikin da sai nan da shekaru 8 za a kammala. Kuma har a rufe ido, tashin farko a kauce wa bin doka da sharuɗɗa wajen bayar da kwangilar.

Da tattalin arzikin mu garau yake, to babu dalilin da zai sa kuma wannan gwamnati ta fara saƙa da mugun zare, ta hanyar kwaikwayon gwamnatin da ta gabata wajen yawan ciwo basussuka.

Harkokin ilmi sun taɓarɓare, haka fannin kiwon lafiya. Ba mu da asibiti ko guda ɗaya a ƙasar nan wanda za mu iya tutiya da shi. An kasa bai wa jami’o’i Naira biliyan 220 da suke buƙata duk shekara domin su farfaɗo, tun 2009.

A halin yanzu ‘yan Najeriya sun afka cikin bala’in tsada da walahar fetur, wadda ba a taɓa fuskantar irin ta ba a baya. Gwamnatin Tinubu ta kasa ba masu hada-hadar fetur Naira biliyan 200 da suke bi bashi, kuɗin cike gurbin bambancin farashi da suke bin gwamnatin bashi.

Sannan kuma ɗanyen mai da Najeriya ke haƙowa, ya ragu zuwa lita miliyan 1.23 a kullum, kamar yadda OPEC ta tabbatar a cikin watan Maris.

PREMIUM TIMES ta yi amanna cewa a wannan lokaci da tattalin arziki ke fama da hawayen kasa kasa tashi tsaye, hanci ke zubar da jini bayan ya sha kutufo da naushin da Dala ke yi masa, guyawun sa sun sage bayan ya sha duka da gora-mai-kaca, tilas a samo wurare masu muhimmanci da za a sa kuɗaɗe domin tattalin arziki ya bunƙasa, amma ba a wurin aikin gina titinan bakin gaɓar ruwan Legas zuwa Kalaba ba.

A halin yanzu ana bin Najeriya bashin Naira tiriliyan 77. Kuma kashi 96 bisa 100 na kuɗaɗen shigar ƙasa duk wajen biyan bashi suke tafiya.

Babban laifi ne a irin wannan yanayi a yi watsi da sauran lalatattun titina, ƙiri-ƙiri kuma a kinkimo wani aikin gina manyan tituna, wanda aka bayar da kwangilar sa a cikin duhu.

People are also reading