Home Back

Karon farko mace na shirin lashe zaben shugaban kasar Mexico

dw.com 2024/7/5
Hoto: Fernando Llano/AP Photo/picture alliance

Claudia Sheinbaum ta kama hanyar zama mace ta farko da aka zaba a matsayin shugabar kasar Mexico, bayan samun kashi 58 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben da aka gudanar ranar Lahadi.

Wadda ke biye mata a matsayi na biyu da kashi 29 cikin 100 na kuri'un ita ma mace, mai suna Xochitl Galves, fitacciyar 'yar kasuwa kuma 'yar majalisar dattijai yanzu haka.

Wanda ke a mataki na uku ne dai namiji mai suna Jorge Alvarez Maynez, mai kashi 11 cikin 100 na kuri'n zaben.

People are also reading