Home Back

ALBASHI: ‘A riƙa biyan Gwamnoni da Sanatoci Naira 62, don su ji irin raɗaɗin da talakawa ke ji a jikin su’ – Gwamna Soludo

premiumtimesng.com 2024/6/26
Soludo ya lace kananan hukumomi 10 cikin 11 da aka bayyana

Gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra, ya ce kamata ya yi gwamnoni da duk masu riƙa muƙaman da talakawa suka zaɓa kan mulki, su koma karɓar mafi ƙanƙantar albashi, domin su ji irin raɗaɗin tsadar rayuwar da ƙananan ma’aikata da talakawa ke ji a jikin su.

Soludo ya yi wannan kira ne a ranar Laraba, a wurin wani taro a Legas, wanda aka gudanar domin cikar Najeriya shekaru 25 da komawa kan turbar dimokraɗiyya.

Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Soludo, Christian Aburime ne ya turo wa PREMIUM TIMES cikakken jawabin Gwamna Soludo a wurin taron.

Soludo ya ce, “irin yadda wasu shugabannin da talakawa suka zaɓa ke ɓalle bushasha da taɓargaza, su na nuna cewa kamar tattalin arzikin Najeriya garau yake.

“Ya kamata mu fito mu faɗa wa ‘yan Najeriya gaskiya, kuma mu riƙa yin abin da ya dace. Najeriya babu kuɗi. Yakamata talakawa su san wannan. Amma fa irin yadda shugabannin da talakawa suka zaɓa da kan su ke bushasha da almubazzaranci da kuɗaɗe, haka ne su na nuna wa talakawa cewa tattalin arzikin Najeriya garau yake.”

“Talakawa na fama da yunwa, kuma sun fara hasala. Kada mu kai su maƙurar bango, kuma mu daina raina masu wayau da hankali. Na yarda da Rabaran Mbaka da ya ce su ma gwamnoni kamata ya yi a riƙa ba su mafi ƙanƙantar albashi. Na yadda a riƙa biyan mu mafi ƙanƙantar albashi, don mu ji irin raɗaɗin rayuwar da talakawa ke fuskanta.” Cewar Soludo.

A farkon wannan mako ne dai NLC da TUC sun tsine wa Naira 62,000, suka ce an maida su mayunwata.

Gamayyar Ƙungiyoyin Ƙwadago na NLC da TUC sun yi tir tare da watsi da ƙarin Naira 2,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi wa mafi ƙanƙantar albashi, zuwa Naira 62,000.

Cikin wata tattaunawa mai zafi da gidan talabijin na Channels TV ya yi da Mataimakin Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), Chris Onyeka, a safiyar Litinin ɗin nan, ya bayyana cewa ba za su taɓa tsayawa sake zaman sulhun amincewa da Naira 62,000 ba.

Ya ce ai “Naira 62,000 sai dai a ba mayunwaci ladar maganin yunwa kawai.”

Idan ba a manta ba, Gwamnatin Tarayya ta amince da yi wa Naira 60,000 ƙarin Naira 2,000 kacal.

Ana wannan ƙaƙuduba ce daidai lokacin da Majalisar Dattawa ta amince wa Shugaba Bola Tinubu ya yi wa alƙalai ƙarin albashi, inda aka ruɓanya masu nunki uku (300%).

A ranar Lahadi ce kuma mai wa’azin addinin Kirista, ɗan taratsi, Rabaran Mbeki, ya bada shawarar a maida albashi gwamnonin Najeriya Naira 62,000, tunda sun ce ba su iya biyan haka a matsayin mafi ƙanƙantar albashi.

Cikin makon jiya ne dai bayan Shugaba Tinubu ya ɗora Naira 2,000 kan Naira 60,000, Gwamnonin Najeriya suka ce 60,000 ɗin ma ba za su iya biya ba.

Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), ta ce maganar gaskiya biyan Naira 60,000 mafi ƙanƙantar albashi ba abu ne mai iya ɗorewa a wajen su ba.

Daraktan Riƙo na NGF a fannin yaɗa labarai, Halima Ahmed ce ya bayyana haka a Abuja, ranar Juma’a.

Sai dai kuma ta ce gwamnonin su na taya ƙungiyoyin ƙwadago damuwa dangane da matsalar rashin wadataccen albashi da ke damun ma’aikatan tarayya, jihohi da na ƙananan hukumomi.

“Idan aka ce jihohi su riƙa biyan Naira 60,000 mafi ƙanƙantar albashi, to fa duk kuɗaɗen da ake raba wa jihohi daga tarayya, wajen albashi za su tafi, ba za a iya rage kuɗaɗen da za a yi sauran ayyuka ba.

“Domin wasu jihohin ma sai sun haɗa da ciwo bashi domin su riƙa biyan jihohin su.”

Ƙarin Albashi: Matsayar Majalisar Tarayya:

‘A Daina Yaudarar Jama’a, Ba Wanda Ke Iya Dogara Da Albashin Sa A Najeriya’:

A zaman Majalisar Tarayya na ranar Laraba, ta koka kan yadda dambarwar ƙarin albashi ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa tsawon shekaru da dama.

Mambobin majalisa da yawa ɗaya bayan ɗaya sun yi kira da a daina maganar ƙarin mafi ƙanƙantar albashi, maimakon haka, a yi maganar ƙarin wadataccen albashin da zai ishi ma’aikata.

Ɗan Majalisar Tarayya Ali Madaki, ɗan NNPP daga Kano, ya jawo ayoyi a cikin Kundin Dokokin Najeriya, inda ya nuna wajibcin yi wa ma’aikata ƙarin albashi wadatacce.

Shugaban Marasa Rinjaye, Kingsley Chinda, ɗan PDP daga Jihar Ribas, ya ragargaji gwamnatin tarayya dangane da rashin ɗaukar albashin ma’aikata da muhimmanci.

“Shin Gwamnatin Tarayya ta na cika aikin da ya wajaba a kan ta. Shin muna samar da tsaro? Shin muna samar da kayan rayuwar jin daɗi ga al’umma? Amsa ita ce ‘a’a’.

“Tsawon shekaru da dama kenan, ana ta magana kan mafi ƙanƙantar albashi, maimakon a yi batun ƙarin wadataccen albashi. Gaskiyar magana babu ma’aikatacin da ke iya dogara da albashin sa kaɗai don ya rayu.

“Ta yaya ma’aikaci zai iya yin aiki ana biyan sa Naira 50,000.00 a wata? Nawa zai biya kuɗin mota zuwa wurin aiki?”

Ƙarin Albashi: Matsayar Ƙungiyoyin Ƙwadago:

‘Ba Za Mu Amince Da Ƙarin ‘Yan Dubunnai Kan Naira 60,000 Ba’:

Bayan janye yajin aiki dai Ƙungiyar Ƙwadago ta ce ba za ta amince Gwamnati ta ƙara ‘yan dubunnai kan Naira 60,000 da ta yi ba.

Yayin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bai wa Ministan Harkokin Kuɗaɗe umarnin sa’o’i 48 ya kai masa ƙarin kuɗin mafi ƙanƙantar albashi domin ya sa hannu, Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC ta bayyana cewa ba fa za ta amince a yi ƙarin wasu ‘yan dubunnai a kan Naira 60,000 ɗin da Gwamnatin Tarayya ta ƙara ba, kafin tafiya yajin aiki.

Shugaban Ƙungiyar TUC, Festus Osifo ne ya bayyana haka, ranar Litinin cikin wata tattaunawar da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.

Ya ce su ba wai sun tsaya lallai sai Naira 494,000 za a biya a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ba. “To amma dai gwamnati ta yi wani abin a zo a gani, wanda kowa zai iya cewa ta yi nata ƙoƙarin.” Inji shi.

Da aka tambaye shi adadin da ya kamata gwamnati ta biya matsayin mafi ƙanƙantar albashi sai ya ce, “ya kamata dai kwamitin gwamnatin tarayya ya fito da wani adadi wanda zai tafi kafaɗa da kafaɗa da halin da tattalin arzikin ƙasa da masifar tsadar kayan abincin da ake fuskanta.

“Saboda mun shaida masu ba za mu amince da irin ƙarin Naira 1, Naira 2 ko Naira 3,000 uku kamar yadda ta riƙa yi a baya ba. Sannan daga nan sai ta riƙa alƙawarin da ta san ba iya cikawa za ta yi ba.”

Ya ce ƙarin albashin da za a yi tilas sai ya yi daidai da abin da Naira 30,000 za ta iya saye a 2019 da kuma abin da Naira 18,000 za ta iya saye 2014.

NLC da TUC dai sun bai wa gwamnatin tarayya kwanaki biyar domin a sami tsayayyen farashi, ko kuma su ci gaba da yajin aiki.

People are also reading