Ci Rani: An Dawo da Yan Najeriya 155 Legas daga Libya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Ikeja, Lagos-Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta bayyana cewa an dawo da yan ci rani 155 da su ka makale a Libya.
Hukumar NEMA ta ce an samu nasarar dawo da mutanen ne ta cikin shirin hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) a jiya Talata.
Kamar yadda ta wallafa a shafinta na X @nemanigeria, hukumar ta ce jirgin Al Buraq ne ya dauko yan Najeriya, kuma ya sauke su a filin jirgin Murtala Muhammed da ke Ikeja, babban birnin Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga mutanen da hukumomin NEMA da IOM su ka yi nasarar dawo da su gida Najeriya akwai mata da maza da kananan yara.
A rahoton da Leadership News ta wallafa, yawan matan ya kai 111 aka dawo da su Najeriya, wanda ke nuna cewa mata da yawa na tafiya ci rani.
Sai kuma jarirai 4, yara 11 da maza 29 da aka dauko daga sassa daban-daban na Libya.
A cewar hukumar NEMA, duk wadanda su ka samu biyo jirgin sun yi murna kwarai da ceto su daga mummunan yanayin da aka yi.
Mun kawo mu ku a karon farko cikin shekaru 25 cewa mace ta zama shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA), wanda hakan ya ja hankali sosai.
Nadin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Zubaida Umar ya ba ta damar zama mace ta farko da ta shugabanci hukumar tun 1999.
Asali: Legit.ng