Home Back

Mun ware miliyoyin Kuɗaɗe domin saɓunta katanga da gyare-gyare a gidan Sarki na Nassarawa – Gwamnatin Kano

dalafmkano.com 2024/6/30

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta ware kuɗi sama da Naira Miliyan 99, domin saɓunta katanga da gyare-gyare a gidan Sarki da ke Nassarawa, bisa yadda gidan ya ɗauki lokaci ba tare da anyi masa wani gyara ba.

Kwamshinan yaɗa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Ɗantiye, ne ya yi wannan jawabin a daren Asabar, yayin kammala taron majalisar zartarwa da gwamnatin jihar ta gudanar domin tattauna batutuwan da suka shafi gwamnati.

Baba Halilu Ɗantiye ya kuma ce, bisa la’akari da yadda gidan Sarkin na Nassarawa ya shafe wasu tsawon shekaru ba tare da gyara ba, ya sanya Majilisar zartarwas ta amince da a ware wannan kuɗaɗen domin sabunta gidan.

Kwamshinan ya ƙara da cewa, yanzu haka gwamnatin ta kara ware makuɗan kuɗaɗe domin biyan malaman jami’o’in Yusuf Maitama Sule da jami’ar kimiyya da fasaha dake Wudil kuɗaɗen da suke bin tsohuwar gwamnati jihar Kano.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, adadin kuɗaɗen da gwamnatin ta ware sama da Biliyan 8 a zamanta na ranar Asabar, domin gudanar da ayyuka daban-daban a ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar Kano.

People are also reading