Home Back

YUNƘURIN ƘIRKIRO ‘ƳANSANDAN JIHOHI: Yaudarar shugabannin Arewa ne na marawa Yarabawa burinsu na cin gashin kai, Daga Ahmed Ilallah

premiumtimesng.com 2024/4/29
BINCIKEN ƘWAƘWAF: Yadda Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi ragabzar kwangilar naira biliyan 3 ba bisa ƙa’ida ba
Nigerian police

Wai shin irin su kungiyar tsaro irin su HISBA, AMETAKUN, VIGILANTE da ma irin Yan Sandan Sarauniya mene aikin su ne? Koma menene, ya kamata Shugabannin Arewa su yi karatun ta natsu, kafin su bi yarima wajen amincewa da ƙirkiro da ƴansandan Jahohi.

Amincewa da kirkirar ƳanSandan Jihohi wani cikar burin Yankin Yarabawa ne, na cin gashin Kansu. Domin sun jima da tsarin gina tattalin arzikin su, wanda a yanzu suka yi wa sauran ƴankunan kasar nan fintinkau.

Samar da ƳanSandan Jihohi ko yankunan cikar burin Yarabawa ne, musamman a yanzu da suke da dama.

Shin Shugabanni da mutanen Arewa wace fahimta suka yi wa kalaman da Sunday Igboho, Shugaban awaren kafa kasar Yarabawa ya yi a kan tsohon Shugaban kasa Shugaba Buhari, zarge zarge da mummunan fatan da yayi masa, da kuma Kiran da yayi na cewa lokaci ya yi Yarabawa su tashi su nemawa kansu cin gashin kai da kubuta daga hannu ƳanArewa Makiyaya, Yanta’adda. Abin kaico din yayi kalamun nan ne fa a Fadar Sarkin Oyo.

Farkon adashen da mutanen Arewa za su dauka, bayan tabbatuwar wannan Ƴansandan, shine tsarewa da hana mutanen su na Arewa, musamman ma matasa masu zuwa cirani dama sana’oin zamani shiga Yankunan su. Za a rika yi musu kazafi da jifan ta’addanci.

Shin a yanzu ma, yaya tsakanin makiyayan da ke wannan Yankin da kungiyoyin su irin su AMETAKUN da sauran tsagerin kungiyoyin su? Kai hatta ma mutanen Arewa masu sahihiyar sana’oin su, wa ce barazana ce ba a musu.

Koda yake yunkurin da surutan siyasa a kan bawa jahohi ko yankunan kasar nan damar samar da Yan Sandan su, abu ne da ya dade a na yin su.

Ba dalili na rashin tsaro da ya sanya a ke bukatar wannan Yan Sandan ba, kawai dalilai ne na siyasa, wanda ya samo asali tun samun yancin Nijeriya, da kuma rigingimun cikin gida da suka faru, kama da yakin basasa, rigingimun siyasa da ma yunkurin neman cin gashin kai irin su Biafra da Yoruba Republic.

In har Najeriya da tafi kowace kasa a fadin Africa girman tsaro, da yawan jami’an tsaro suka gaza shawo kan wannan rashin tsaro, ta yaya sabbin Ƴansandan Jihohi zasu kawo.

Kusan fa zamantakewar ƳanNajeriya fa na daga cikin abubuwan da ke musu tarnakin cigaban ta, domin kowane Yankin na da nasa burin a kan Najeriya.

Su fa Yankin Yarabawa burin su shine a kasa Najeriya kowa yaci gashin kansa abin da ake kira decentralization, samar da Yan Sandan Jahohi na daga cikin sa.

Babu wani Yankin da yake komabaya a Najeriyar yau sai Yankin Arewa. Yaki, talauci, komabayan harkar ilimi da lafiya dama zaman lafiya ya damalmale shi.

Babu wata kiyayya a Shugabancin siyasa na baya da na yanzu dan taimakon wannan Yankin.

Kai babu wani tsari, tunani koma hadaka da wannan Yankin ya ke da a bayyane don ciyar da Yankin gaba. Kamar yadda muka ga tsarin Yarabawa a yau, irin DAWN (Development Agenda for Western State.

 
People are also reading