Home Back

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Wasu Kauyukan Neja Bayan Sojoji Sun Janye

legit.ng 2024/5/14
  • Miyagun ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyukan jihar Neja waɗanda mutanen garin suka gudu saboda janyewar sojoji daga yankin
  • Ƴan bindiga sun kwashe kayan abinci a ƙauyen Allawa da waɗanda ke makwabtaka da shi a sabon harin da suka kai
  • Mutanen ƙauyukan duk sun gudu bayan sojoji sun janye daga yankin sakamakon wani harin kwanton ɓauna da aka yi musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Kwanaki uku da janyewar sojoji daga ƙauyen Allawa dake karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, wasu ƴan bindiga sun kai farmaki tare da sace kayan abinci.

Mazauna garin sun tsere ne bayan da sojoji suka janye saboda wani kwanton ɓauna da aka yi musu.

'Yan bindiga sun kwashe kayan abinci a Neja
'Yan bindiga sun sace kayan abinci a kauyukan jihar Neja Hoto: Umaru Bago Asali: Facebook

Ɗaya daga cikin mazauna garin, Malam Yahuza Allawa, ya tabbatarwa jaridar Daily Trust ta wayar tarho kai sabon harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ƴan bindigan sun shiga garuruwan da ke makwabtaka da Allawa da safiyar ranar Lahadi inda suka yi awon gaba da kayan abinci da sauran kayayyaki masu amfani da suka haɗa da awaki da sauran dabbobin gida.

Ya ce mazauna garin Allawa, Saminaka, Gyra-Miyan, Unguwan Sarkin-Noma, Kurmi duk sun gudu tun ranar Alhamis.

Ƴan bindiga sun sace kayan abinci

Mazauna garin sun ce wasu da suka koma gida domin ɗibar kayan abinci sun dawo da rahoton cewa ƴan bindigan sun zo da manyan motoci inda suka kwashi kayan abinci da safiyar ranar Lahadi.

"Ƴan bindigan sun zo da safen nan sun sace abincinmu da sauran kayayyaki har da awakai. Ba mu ɗauki da yawa daga cikin kayanmu ba saboda rashin abun hawa. Sai da mu ka yi tattaki daga ƙauyukanmu zuwa Elena."
"Ƴan bindigan sun zo da babbar mota wacce suka ɗora kayan abincin a ciki. Sun ajiye motar a bakin ruwa sannan suka yi amfani da babura wajen ɗauko kayan daga ƙauyukanmu saboda yanayin hanyar."

- Malam Yahuza Allawa

Asali: Legit.ng

People are also reading