Home Back

BINCIKE: Shin gaskiya Peter Obi ya faɗa cewa gwamnatin Tinubu ta bijire wa umarnin kotu dangane da ƙin sakin Nnamdi Kanu?

premiumtimesng.com 2 days ago
ZAƁEN SHUGABAN KASA: Yadda Peter Obi na LP ya lallasa Tinubu a ƙaramar hukumar sa ta Ikeja

A ranar 29 ga Yuni, ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya yi iƙirarin cewa shugaban IPOB, Nnamdi Kanu na tsare ne a hannun gwamnatin Najeriya, bisa take umarnin kotu.

Peter Obi ya bayyana hakan ga manema labarai a Anacha, cikin Jihar Anambra.

“Ni ban ga dalilin ci gaba da tsarewar da ake yi wa Nnamdi Kanu ba, musamman ganin yadda wasu kotuna suka bayar da belin sa. Tilas gwamnati ta bi umarnin kotu.

“Mulkin dimokraɗiyya ne fa muke. Saboda haka mu daina yin abu ƙarfa-ƙarfa, mu daina tsallake kan iyakokin da doka ta tanadar,” inji Peter Obi.

Ko Tinubu Ya Take Dokar Bada Belin Nnamdi Kanu?

Tinubu ya hau mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, bayan nasarar zaɓen shugaban ƙasa, wanda aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.

An kama Kanu kamun farko cikin 2015, a ƙarƙashin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.

Ana tuhumar Kani da laifin aikata ta’addanci da wasu laifuka daban-daban.

A ranar 13 ga Oktoba, 2022, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja ta ayyana cewa damƙowar da aka yi wa Kanu daga Kenya aka sunƙumo shi cikin jirgi zuwa Najeriya, an tauye masa ‘yanci.

Daga nan kotun ta soke zargin ta’addanci da gwamnatin Najeriya ke yi masa, kuma ta bayar da umarnin a sake shi daga hannun SSS.

Amma bayan sati ɗaya, gwamnatin Najeriya ta hannun Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, ta ɗaukaka ƙara, ta samu umarnin dakatar da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke, daga Kotun Ƙoli.

A ranar 15 ga Disamba, 2023, Kotun Ƙoli ta soke belin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayar kan Kanu, tare da bayar da umarnin sake komawa Babbar Kotun Tarayya, ta Abuja domin ci gaba da shari’ar.

Kotun Ƙoli dai ita ce ƙololuwar ƙarshe a yanke hukunci a Najeriya.

Yanzu haka ana ci gaba da shari’ar.

Batun Zargin Da Peter Obi Ya Yi:

Zargin da Peter Obi ya yi cewa gwamnatin Tinubu ta ƙi sakin Nnamdi Kanu beli kamar yadda kotuna suka bayar da umarni, kwata-kwata babu gaskiya ko kaɗan a kalaman na sa.

People are also reading