Home Back

‘Yan Bindiga Na Sake Hada Gungu Duk Da Farmakin Sojoji

leadership.ng 2024/5/19
Sojoji

Duk da hare-hare gami da fatattakar da sojoji ke yi wa ‘yan bindiga, ga dukkan alamu ‘yan bindigar dake yankin Arewa maso yammacin Nijeriya na ci gaba da hadewa suna kai hare-hare a Maradun da Zuru, a Zamfara da kuma Karamar Hukumar Kankara a Katsina cikin kwanaki 3 da suka gabata.

LEADERSHIP Weekend ta ruwaito daga majiya mai tushe ta rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara cewa kwanaki ukun da suka gabata an fuskanci matsi sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa.

‘Yan bindiga sun kuma kai hari tare da kashe sojoji 6, biyu daga cikinsu jami’ai ne a karamar hukumar Shiroror ta jihar Neja, jihar ta Arewa ta tsakiya wacce ke kan iyaka da Kaduna da Kebbi, dukkansu jihohin Arewa maso Yamma.

Sojojin Nijeriya tare da hadin gwiwar jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun dakile harin ‘yan ta’adda a Jihar Sokoto, inda suka kashe bakwai daga cikin ‘yan ta’addan.

A wata sanarwa da rundunar sojin Nijeriya ta fitar akan shafinta na D ta ce dakarun da ke jiran ko-ta-kwana sun kama wasu ‘yan ta’adda dauke da makamai a wani farmaki da suka kai a yankin Modachi na Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato.

Sanarwar ta ce dakarun da ke aikin hadin gwiwa sun kashe 7 daga cikin ‘yan ta’adda tare da kwato manyan tarin makamai.

‘Yan ta’adda da ke wucewa da babura da dama, jami’an tsaro sun yi artabu da su, lamarin da ya kai ga halaka ‘yan ta’adda bakwai.

Sannan Sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 bakwai, babura hudu, wayoyin hannu biyu, da adduna hudu.

Sojojin Nijeriya a cikin makonni uku da suka gabata sun kashe ‘yan ta’adda 31 a yankin Arewa maso Yamma, gami da kwato wasu makamai tare da rasa sojoji 7 a wani harin kwantan bauna.

A harin na baya-bayan nan, an bayyana cewa wasu ‘yan bindiga a Katsina sun kashe wani jami’in runduna ta 17 na sojojin Nijeriya, Manjo A.G Mohammed.

Marigayi Mohammed mamba ne na Operation Hadarin Daji kuma kwamandan da ke kula da ayyukan soji a Bantumaki, Dan Ali da Kankara a jihar.

People are also reading