Home Back

Gwamnatin Kano Ta Yiwa Tashar Arewa 24 Babban Alkawari Bayan Cika Shekaru 10

legit.ng 2024/8/23
  • Tashar talabijin Arewa 24 ta yi bikin cika shekaru 10 da fara watsa shirye-shirye daban-daban a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya
  • Gwamnatin jihar Kano ta yabi tashar Arewa 24 bisa kokarin da suke tare da musu babban alkawari domin haɓaka shiryen-shiryensu
  • Duk da haka, gwamnati ta yi hannunka mai sanda kan wasu shiryen-shiryen da gidan talabijin din ke yaɗawa a Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta yi alkawarin taimakawa wajen inganta shiryen-shiryen da tashar Arewa 24 ke yi.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kuma yabi tashar kan shirye shiryen masu kyau da suke yaɗawa.

Jihar Kano
Gwamnatin Kano za ta tallafawa Arewa 24. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne a cikin wani biyo da mai taimakawa gwamnan Kano kan harkokin sadarwa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkawarin gwamnatin Kano ga Arewa 24

Mai taimakawa gwamnan jihar Kano kan harkokin sadarwa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya bayyana cewa Kano na shirye wajen tallafawa Arewa 24.

Sanusi Bature ya tabbatar da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta tallafi Arewa 24 wajen samar da hedikwata a jihar Kano.

Kiran gwamnatin Kano ga tashar Arewa 24

A yayin bikin, gwamnatin Kano ta yi kira na musamman ga tashar Arewa 24 kan bada horo ga ma'aikata talabijin din jihar.

Gwamnatin ta ce hakan zai taimaka wajen samar zaratan ma'aikata da kuma yin aiki yadda ya kamata.

Gwamnatin Kano ta yabi Arewa 24

Mai magana da yawun gwamnatin Kano, Sanusi Bature ya yabi tashar Arewa 24 bisa saka shirye-shiryen da suke tallata al'adun Hausawa.

Sai dai duk da haka ya ce akwai wasu shirye-shirye da ya kamata su saka labule domin ganin an kawo gyara kan yadda ake gudanar dasu.

Kotu ta daga shari'ar sarautar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake ci gaba da rigima kan kujerar sarautar Kano, kotu ta ɗage zaman ƙarar da gwamnatin Kano ta kai kan tsige Aminu Ado Bayero.

Mai Shari'a Amina Adamu Aliyu ta ɗage ƙarar da aka nemi hana Aminu Bayero da sarakuna hudu ayyana kansu a matsayin sarakuna zuwa nan gaba kadan.

Asali: Legit.ng

People are also reading