Home Back

Fadar Sarkin Musulmi Ta Bayyana Gaskiya Kan Rigima da Gwamnatin Sokoto

legit.ng 3 days ago
  • Fadar Sarkin Musulmi ta fito ta yi magana kan batun da ake yaɗawa cewa akwai saɓani a tsakaninta da gwamnatin jihar Sokoto
  • Fadar ta bayyana cewa babu wata matsala a tsakanin mai alfarma Alhaji Sa'ad Abubakar III da gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu
  • Sa'in Kilgoro wanda ya tabbatar da hakan ya ce a shirye fadar Sarkin Musulmin take ta yi aiki da sabuwar dokar da ake ƙoƙarin kawowa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Daga ƙarshe fadar Sarkin Musulmi ta yi magana kan batun gyaran dokar ƙananan hukumomin jihar Sokoto ta shekarar 2008.

Sa’in Kilgori, Dakta Muhammad Jabbi Kilgori, ya ce gyaran da za a yiwa dokar ba zai ƙwace iko ko rage ƙarfin da Sarkin Musulmin yake da shi ba.

Fadar Sarkin Musulmi ta musanta samun sabani da gwamnan Sokoto
Fadar Sarkin Musulmi ta shirya aiki da sabuwar doka a Sokoto Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wajen buɗe taron jin ra'ayin jama'a kan gyaran da za a yiwa dokar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai matsala tsakanin Sarkin Musulmi da gwamna?

Ya bayyana cewa saɓanin abin da ake yaɗawa, babu wata matsala tsakanin Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III da gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu.

Dakta Muhammad Jabbi Kilgori, wanda yake da muƙamin Hakimin Kilgori kuma mamba a majalisar Sarkin Musulmi, ya ce fadar na sane da wasu maƙiya masu son kawo matsala tsakanin Sarkin Musulmi da gwamnatin jihar.

"Babu wata matsala tsakanin Sarkin Musulmi da Gwamna Ahmed Aliyu. Majalisar Sarkin Musulmi a shirye take ta yi aiki da kowace doka wacce aka samar ta hanyar da ta dace."
"Mun yi aiki da dokoki daban-daban a baya kuma a shirye muke mu yi aiki da wannan sabuwar dokar."
"Majalisar Sarkin Musulmi ta yi aiki a ƙarƙashin dokar da ake shirin yiwa gyara na tsawon shekara 16. A shirye muke mu yi aiki tare da gwamnati."

- Dakta Muhammad Jabbi Kilgori

Batun tsige Sarkin Musulmi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta musanta zargin da MURIC ta yi na cewa tana shirin tsige mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Ta kuma buƙaci mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da ya riƙa bin diddigin gaskiya kafin ya yi tsokaci kan wasu muhimman batutuwan da ke faruwa a ƙasa.

Asali: Legit.ng

People are also reading