Fadar Sarkin Musulmi Ta Bayyana Gaskiya Kan Rigima da Gwamnatin Sokoto
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Daga ƙarshe fadar Sarkin Musulmi ta yi magana kan batun gyaran dokar ƙananan hukumomin jihar Sokoto ta shekarar 2008.
Sa’in Kilgori, Dakta Muhammad Jabbi Kilgori, ya ce gyaran da za a yiwa dokar ba zai ƙwace iko ko rage ƙarfin da Sarkin Musulmin yake da shi ba.
Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wajen buɗe taron jin ra'ayin jama'a kan gyaran da za a yiwa dokar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa saɓanin abin da ake yaɗawa, babu wata matsala tsakanin Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III da gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu.
Dakta Muhammad Jabbi Kilgori, wanda yake da muƙamin Hakimin Kilgori kuma mamba a majalisar Sarkin Musulmi, ya ce fadar na sane da wasu maƙiya masu son kawo matsala tsakanin Sarkin Musulmi da gwamnatin jihar.
"Babu wata matsala tsakanin Sarkin Musulmi da Gwamna Ahmed Aliyu. Majalisar Sarkin Musulmi a shirye take ta yi aiki da kowace doka wacce aka samar ta hanyar da ta dace."
"Mun yi aiki da dokoki daban-daban a baya kuma a shirye muke mu yi aiki da wannan sabuwar dokar."
"Majalisar Sarkin Musulmi ta yi aiki a ƙarƙashin dokar da ake shirin yiwa gyara na tsawon shekara 16. A shirye muke mu yi aiki tare da gwamnati."
- Dakta Muhammad Jabbi Kilgori
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta musanta zargin da MURIC ta yi na cewa tana shirin tsige mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.
Ta kuma buƙaci mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da ya riƙa bin diddigin gaskiya kafin ya yi tsokaci kan wasu muhimman batutuwan da ke faruwa a ƙasa.
Asali: Legit.ng