Home Back

Hajj 2024: Gwamna Abba Yusuf Ya Nada Sabon Amirul Hajjin Jihar Kano

legit.ng 2024/6/18
  • Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin ba kowanne maniyyacin jihar kyautar $500 a matsayin alawus yayin da za su je sauke farali
  • Gwamna Abba Yusuf ne ya sanar da hakan a lokacin da ya halarci taron bitar da aka yi wa mahajjatan a sansanin alhazai na jihar
  • Haka zalika, mai girma Abba Yusuf, ya nada mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam a matsayin Amirul Hajj na Kano a bana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya nada sabon Amirul Hajj da zai jagoranci maniyyata aikin Hajjin Kano zuwa kasa mai tsarki domin sauke farali.

Abba Yusuf ya nada mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam a matsayin Amirul Hajj na jihar a bana.

Gwamna Abba Yusuf ya nada Amirul Hajj na jihar Kano
Kano: Gwamna Abba Yusuf ya nada Amirul Hajj na bana. Hoto: @Kyusufabba Asali: Twitter

Gwamnan wanda ya sanar da hakan a shafinsa na X ya kuma yi alkawarin gwangwaje maniyyatan jihar da kyautar dala 500 kowanne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a ba mahajjan Kano kyautar $500

A jiya Litinin, mai girma Abba ya halartar bitar aikin Hajji da aka yi wa maniyyatan Kano, wanda aka yi a sansanin alhazai na jihar.

A cewar Gwamna Yusuf:

"Na yi amfani da wannan damar domin sanar da cewa kudin alawus na tafiye-tafiye ga maniyya zai zama $500 idan farashin Dala a kan Naira ya na a N1,250/$1.
"Mun yi wannan karamcin ne domin baiwa mahajjata damar gudanar da aikin Hajji ba tare da wata matsala ba."

An nada Amirul Hajj na Kano

Game da nadin Amirul Hajj na bana, gwamnan jihar na Kano ya ce:

"Na kuma sanar da cewa mataimakin gwamnan jihar, H.E Aminu Abdulsalam ne zai jagoranci tawagar gwamnatin jihar da alhazai zuwa aikin hajjin bana.
"Ina yi wa dukkanin mahajjata fatan alheri da kuma yin wannan tafiya cikin nasara."

Karanta sanarwar a kasa:

Gwamna Fintiri ya nada Amirul Hajj

A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya nada sabon Amirul Hajj na jihar.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, mai girma Ahmadu Fintiri ya amince da nadin Mustapha Amin, Galadiman Adamawa a matsayin Amirul Hajji na jihar.

Asali: Legit.ng

People are also reading