Home Back

A Tsarin Mulki, Sarkin Musulmi Ba Shi Da Ikon Naɗa Wani – Gwamnatin Sokoto

leadership.ng 2 days ago
A Tsarin Mulki, Sarkin Musulmi Ba Shi Da Ikon Naɗa Wani – Gwamnatin Sokoto

Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa Sarkin Musulmi ba shi da hurumin naɗa wasu muƙamai a tsarin mulki. A yayin wani taron jin ra’ayin jama’a kan dokar ƙananan hukumomi da masarautu ta Sakkwato na shekarar 2008, kwamishinan shari’a Barista Nasiru Binji ya bayyana cewa dokar da aka kafa ta sarakunan gargajiya ta ci karo da tsarin mulkin Najeriya.

Barista Binji ya bayyana cewa sashi na 76(2) na dokar ƙananan hukumomi da masarautu na Sokoto ya saɓawa sashe na 5(2) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999, wanda ya ba da ikon zartarwa, ciki har da naɗe-naɗen mukamai a Gwamnatance, da kai tsaye ko ta hanyar wakilai, da kwamishinoni. ko wakilan gwamnati da aka naɗa.

“Sashen ya bai wa majalisar Sarkin Musulmi ikon naɗa hakimai da gundumomi tare da amincewar Gwamna, wanda hakan ya saba wa kundin tsarin mulki,” in ji shi, inda ya jaddada cewa yanzu ana neman gyara kura-kuran da aka yi a baya ta hanyar daidaita dokar jihar da tanade-tanaden kundin tsarin mulki.

Bugu da kari, ƙudurin dokar ya ba da shawarar tsawaita wa’adin shugabannin ƙananan hukumomi zuwa shekaru uku domin inganta aikinsu.

People are also reading