Home Back

‘Yan Bindiga Sun Sace Malaman Jami’ar Jihar Katsina

leadership.ng 2024/7/3
‘Yan Bindiga Sun Sace Malaman Jami’ar Jihar Katsina

Wasu ‘yan bindiga sun sace wasu malaman jami’ar tarayya ta Dutsin Ma da ke jihar Katsina, Farfesa Richard Kyaram da kuma Dakta Hamza.

An samo cewa, an sace Mista Kyaram ne tare da dansa, Solomon.

Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a GRA Dustin Ma da misalin karfe 1:am na ranar Litinin.

An kuma rahoto cewa, ‘yan ta’addan sun afka GRAn ne da muggan makamai inda suka rika harbe-harbe a sama.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yansandan jihar Katsina, Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin. Sai dai, ya ce, rundunar tana aiki tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro domin ceto wadanda aka sacen.

People are also reading