Home Back

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya

bbc.com 2024/5/18

Rahoto kai-tsaye

Jam'iyyar da ke mulki a Togo ta lashe zaben 'yan majalisar dokoki

A

Asalin hoton, .

Jam'iyyar da ke mulki a Togo ta lashe zaben 'yan majalisar dokoki da gagarumin nasara, wanda hakan zai bai wa shugaba Faure Gnassingbe damar cigaba da zama a mulki.

Sakamakon wucin-gadi da aka fitar ya nuna jam'iyyar UNIR ta samu kujeru 108 cikin 113 da ake da su a majalisa.

Kuma dama dokokin sabon kudin tsarin mulkin kasar da aka yiwa kwaskwarima a watan daya gabata, majalisa ce ke da hurumin zaben shugaban gwamnati, sauyin da masu adawa suka yi alla-wadai da shi, tare da bayyana cewa wani salo ne na bai wa iyalan Gnassingbe damar cigaba da mulki na har abada.

People are also reading