Home Back

Sabon salon ƴan bindiga na tilasta wa mutane saya musu babur

bbc.com 2024/4/29
Ƴan bindiga

Asalin hoton, AFP

A baya-bayan nan wane abu da yake fitowa fili shi ne na yadda ƴan bindiga ke tilasta wa mutane saya musu babur a matsayin fansa kafin su saki ƴan uwansu da suka kama.

Ana iya cewa hakan dai ba ya rasa nasaba da toshe musu hanyar sayan babur ɗin da hukumomi suka yi, duk a ƙoƙari da ake yi wajen dakile ayyukansu.

Ƴan bindiga dai na ci gaba da cin karensu babu babbaka a arewacin Najeriya, musamman ma yankin arewa maso yamma.

Matsalar dai na ta ƙara ta'azzara a baya-bayan nan duk da irin matakan da hukumomi ke cewa suna ɗauka na kawo karshen ƴan bindigar.

Yanzu dai babu wanda ya tsira kama daga mai kuɗi da kuma talaka, inda ake yin garkuwa da kowaye don neman kuɗin fansa.

A ɗan tsakanin nan, ƴan bindigar sun koma far wa masallatai, musamman ma a wannan lokaci na azumi yayin da mutane ke yin ibadoji, inda suke yin awon gaba da masu ibada.

Wani ganau wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana wa BBC cewa hakan ta faru kan wani ɗan uwansa da kuma abokanayensa.

“ Yanzu bayan sun ɗauke ka dole ne bayan ka gama biyan kuɗin fansa dole ne sai ka saya babur ka ka musu.

“Akwai Boxer wanda kuɗinsa ya kai naira 960,000, akwai kuma Honda wanda shi ma ya kai kusan miliyan biyu,” in ji ganau ɗin.

Ya ce ƴan bindigar na amfani da baburan ne wajen tafiya mai nisa don aikata miyagun laifuka.

Ya ce su kaɗai suke amfani da baburan saboda sun fi karfin talaka ma ya saye su.

Ya ƙara da cewa muddin ba a sayi babur ba to fa ba za su saki wanda suka yi garkuwa da shi ba.

“In ba a kai babur ba za su iya komawa garin su sake kwasar mutane wanda ka ga dole sai an saya,” in ji shi.

Ya ce wannan abu na faruwa ne a karamar hukumar Faskari na jihar Katsina, inda ya ce suna cikin tashin hankali sun kuma rasa yadda za su yi da rayuwarsu.

Ya kira ga gwamnan jihar da ya kawowa kauyukan Sabon Layin Galadima, Unguwar Tsamiya, Birnin Kogo, Mai Gora da sauransu.

Yaya masana tsaro ke kallon sabon salon ƴan bindigar?

Dakta Kabiru Adamu, masani kan harkar tsaro, ya ce wannan dai ba sabon abu bane, musamman a arewa maso gabas.

Ya ce hakan yana nuna cewa baburan suna da muhimmanci a wajen ƴan bindigar domin suna saukaka musu wajen tafiya.

“Wani abu kuma shi ne sun rena hukuma ta yadda ko sun gabatar da buƙatar hakan ba dole ne a cimmusu ba,” in ji Dr Kabiru Adamu.

Ya ce yana iya yiwuwa ƴan bindigar sun ƙara samun sabbin mambobi ne ya sa suke buƙatar neman a saya musu babur ko kuma waɗanda suke da su sun fara lalacewa.

Dakta Adamu ya yi kira ga al’umma da su ƙara buƙatar hukuma ta sauke hakkin da ke kanta na kare rayua da kum dukiyoyinsu.

“A matsayin mu na al’umma mu haɗu da murya ɗaya ba tare da ɓatanci ko zagi ba, mu buƙaci hukuma ta ɗauki matakin da ya dace,” in ji shi.

 
People are also reading