Home Back

Gwamnonin Arewa Maso Yamma Sun Lashi Takobin Kawo Karshen Matsalar Tsaro

leadership.ng 3 days ago
Gwamnonin Arewa Maso Yamma Sun Lashi Takobin Kawo Karshen Matsalar Tsaro

Kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Yamma, ta kafa wani kwamiti da zai rika tuntubar juna da aiwatar da abubuwan da aka cimma bayan, kammala taron inganta zaman lafiya da tsaro a yankin da aka gudanar a Jihar Katsina.

An gudanar da taron ne da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya.

Kwararru da sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro sun tattaunawa na tsawon kwana biyu tare da cimma matsaya kan abubuwa da dama wadanda za su taimaka wajen magance matsalar tsaron da ke addabar yankin.

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ne, shugaban kungiyar gwamnonin Arewa Maso Yamma, kuma ya bayyana cewar taron ya bambanta da wanda suka sha yi a baya.

Ya ce ganin irin fuskokin da suka halarci taron, hakan ya nuna musu cewar matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin ta dami kowa, wanda yasa mutanen da a baya suke yi wa lamarin rikon sakaci, yanzu kowa ya fahimci cewar dole ne a hada hannu wajen ganin an dauki matakai da za su kawo karshen matsalar.

A baya dai gwamnonin yankin, sun sha gudanar da zama iri daban-daban dangane da sha’anin tsaro wanda ke ci gaba da kawo koma baya ga yankin.

People are also reading