Home Back

Tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde Ya Rasu

leadership.ng 2024/9/28
Tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde Ya Rasu

Tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Lamorde ya rasu.

Lamorde ya rasu yana da shekaru 61 a duniya.

Wata majiya daga iyalansa ta ce, Lamorde ya rasu ne a Masar (Egypt) a ranar Lahadi inda yake jinya

An haife shi a ranar 20 ga Disamba 1962, Lamorde ya kuma shiga aikin ‘yansandan Nijeriya a shekarar 1986 kuma ya yi ritaya a matsayin mataimakin babban sufeton ‘yansanda a shekarar 2021.

Lamorde ya rike mukamin shugaban hukumar EFCC tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.

Lamorde shi ne Shugaban Hukumar na uku. An nada shi a matsayin shugaban hukumar a ranar 3 ga watan Nuwamba 2011 bayan da shugaba Goodluck Jonathan ya tsige Farida Waziri. Majalisar dattijai ta tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar na uku a ranar 15 ga Fabrairu 2012.

Lamorde, an haife shi ne a ranar 20 ga Disamba 1962 a Mubi, Jihar Adamawa, ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya kammala digirinsa na farko a fannin ilimin zamantakewa a shekarar 1984. Ya shiga aikin ‘yansandan Nijeriya a shekarar 1986.

People are also reading