Home Back

Gwamnatin Kano Za Ta Dauki Masu Gadi 17,600 Don Bai Wa Makarantun Jihar Tsaro

leadership.ng 3 days ago
Gwamnatin Kano Za Ta Dauki Masu Gadi 17,600 Don Bai Wa Makarantun Jihar Tsaro 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirin daukar masu gadi 17,600 aiki don kare makarantu a fadin jihar. 

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana wannan ci gaba a shafinsa na X a ranar Laraba.

Gwamna Yusuf ya bayyana cewa, “Bugu da kari kan gyare-gyare da gina sabbin ajujuwa, muna shirin daukar masu gadin makarantu 17,600 a fadin jihar Kano. Za a dauki ma’aikatan a fadin jihar nan domin tabbatar da tsaron makarantun firamare, malamai da dalibai, tare da ma’aikata 400 daga kowace karamar hukuma.”

“Shirin na da nufin inganta tsaro a matakin farko, tare da daukar masu gadi daga yankunan da makarantun suke.

Gwamna Yusuf ya kara da cewa, “Za a dauki masu gadin aiki ne daga yankin da makarantun suke don tabbatar da tsaro.”

Wannan sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da Gwamna Yusuf ya bayyana a baya cewa an ware Naira biliyan 1.9 don gyaran ajujuwa a fadin jihar.

Har wa yau, gwamnan ya amince da karin Naira biliyan 2.9 don gina sabbin ajujuwa, inda ya ce, “Wannan shi ne mataki na farko daga cikin yunkurin gina sabbin ajujuwa don inganta ilimi a fadin jihar Kano.”

Duka dai wannan na zuwa ne bayan da Gwamna Yusuf ya bayan ayyana dokar ta baci kan ilimi a ranar 8 ga watan Yuni.

Shirin zai bunkasa ilimi da ababen more rayuwa, da nufin inganta harkar ilimi a Jihar Kano.

People are also reading