Home Back

Shaci-faɗi 10 kan hanyoyin rage ƙiba

bbc.com 2024/5/5
...

Asalin hoton, Getty Images

  • Marubuci, Emma White
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, En association avec Nutracheck

Shin wadanne dabarun rage ƙiba kuka fi so? Cin abinci ko kuma rashin ci, da yawa daga cikinmu suna da hanyoyin da suke bi wajen rage ƙiba cikin sauri.

Abin bakin ciki shi ne, wasu hanyoyi masu sauri da muke bi a kokarin rage kiba tamkar camfe-camfe ne kawai ko kuma shaci-fadi.

Salade

Asalin hoton, Getty Images

Camfi na 1: Adana kayan itace da ganyayyaki don rage kiba

Mutane suna magana game da kyautar abinci, irin su 'ya'yan itatuwa da kayan marmari, waɗanda za a iya watsi da sinadaran da ke cikinsu saboda rashin yawansu. Amma babu abinci "kyauta," saboda duk abinci yana ba mu wani matakin kuzari, kuma idan mun ci isasshen abinci, zai yi tasiri a jikinku.

Idan burinku shi ne rage ƙiba, Ina ba ku shawara ku lura da 'ya'yan itace da kuke ci da kuma ganyayyaki, saboda yana da mahimmanci a yi duba game da abincin ku - ita ce kawai hanyar da za ku iya sanin yawan kuzarin ku. Idan kuna da burin rage ƙiba, kuna buƙatar sanin ainihin abin da kuke ci.

Camfi na 2: Abinci mai ɗauke da sinadaran gina jiki da yawa na rage kiba

Shin karas, masara, ko koren shayi shi ne amsar burinku na rage kiba? Amma babu wani takamaiman abinci ɗaya da zai iya tasiri wajen rage ƙiba.

Tambaya ce mai faɗi: abincinku gaba ɗaya da haɗin waɗannan nau'ukan abinci iri-iri. Nemo wane abinci ne zai iya amfanar lafiyarku gaba ɗaya a cikin labarinmu mai taken "Nau'ukan Abinci Mafi Lafiya 20".

Ba ri mu ce kuna cin abinci mai ɗauke da sinadaran ƙara kuzari 3,000 a rana, amma kuna cin ganyen kabeji guda uku. Za ku iya ƙona kitse da kuma gishiri mai yawa.

Wannan ba yana nufin cewa waɗan nan abincin ba su da fa'ida ko sinadarai masu gina jiki, amma yana da matukar muhimmanci mu ci gaba da mayar da hankali kan abinci mai gina jiki maimakon burin cewa akwai wata mafita kan lamarain - domin kuwa babu mafitar.

Aliments protéinés

Asalin hoton, Getty Images

Camfi na 3: Cin abincin da ke da ƙarancin sinadarin sa kuzari

Tsara yadda za a ci abinci na iya sa a rage kiba. Amma yawancin bincike sun nuna cewa babu bambanci na dogon lokaci.

Ba lallai ba ne a yanke sinadarin carbohydrates, amma rage su ɗan kaɗan da cin ƙarin abinci mai ɗauke da sinadarin protein zai iya taimakawa.

Kawai zaɓi nau'in carbohydrate da ya dace, kamar hatsi.

Camfi na 4: Abinci mai ɗauke da sinadarin protein yana da muhimmanci

Wannan yana tafiya ne hannu da hannu da nau'in abincin da ke da ƙarancin sinadarin sa kuzari, yayin da mutane da ke cin irin abincin, ke maye gurbin abinci mai sinadarin protein da carbohydrates.

Kana buƙatar protein da yawa, sai dai bincike ya nuna cewa cin abinci mai sinadarin protein da yawa, zai janyo rage ɗimbin kiba.

Camfi na 5: Cin abinci mai inganci maimakon mai yawa zai sa ka rage kiba

Ba abun mamaki ba ne cewa mutane da yawa na tunanin cewa yana da muhimmanci a zaɓi lafiyayyen abinci yayin rage kiba.

Gaskiya ne cewa yana da sauki a ɗauki matakin rage cin abinci mai sa kuzari, musamman abinci mai sinadarin protein da ƴaƴan itace da kuma ganyayyaki.

Sai dai, nau'in abinci mai lafiya irin su gyaɗa, mai da kuma kifi na da sinadarin sa kuzari mai yawa.

Idan kuma a ka zo ga batun rage kiba, yana da kyau a rage abinci mai sinadarin ƙara kuzari. Don haka, ya kamata ka san mai kake ci don sanin yanayin da kake ciki.

Homme en surpoids qui mange

Asalin hoton, Getty Images

Camfi na 6: “Nau'in abinci mai gina jiki” shi ne hanyar rage kiba tilo

Zai iya kasancewa cewa, nau'in abinci mai ƙarancin sinadarin ƙara kuzari ya zama zaɓi mai kyau, sai dai ya kamata ka lura da ɗaukacin abincin da kake ci.

Abinci mai ɗauke da sinadarin protein, ƴaƴan itace da kuma ganyayyaki na da muhimmanci ga lafiyarka da kuma samun nasarar ɗorewa kan tsarin cin abinci mai kyau.

Camfi na 7: Dukkanmu mu kan rame wani lokacin

A yawan lokuta ina jin mutane na cewa abokansu na rage ƙiba a kowane mako, duk da cewa suna fuskantar matsala wajen yin haka.

Wannan na faru ne saboda jiki ba na'ura ba ne kuma akwai wasu dalilai da yawa da kan yi tasiri kan irin kuzarin da muke buƙata, ciki har da sassan jiki, zaɓin abinci da kuma gishiri da ke ciki (wanda zai sa jiki ya riƙe ruwa) da kuma rage gajiya.

Lura da wasu nau'o'i, zai sanya ka kasance cikin kuzari ko da ba ka ganin sakamako mai kyau.

Shin kana da kuzari da yawa? Kana jin daɗin abincin da kake ci? Shin tufafinka suna yi maka daidai? Kana barci mai kyau?

Ka kuma tuna cewa batun rage kiba ba shi da mataki zuwa mataki. Idan ka ga wani sauyi, to kana tafiya yadda ya kamata.

Femme qui fait du sport

Asalin hoton, Getty Images

Camfi na 8: Sayen lafiyayyen abinci na da tsada

Mun riga mun yi magana kan cewa ba dole ba ne sayen nau'in abinci na musamman, sai dai mutane da yawa na nuna damuwa cewa sayen sabbin kayan abinci na da tsadar gaske. Za a iya sayen lafiyayyen abinci kan ƙankanin kuɗi.

Ka zaɓi nau'in abincin da za ka iya, musamman ganyayyaki da kuma nau'in abinci na hatsi domin faɗaɗa cimarka da kuma rage kuɗin da kake kashewa yayin da kake inganta yanayin cin abincika.

Camfi na 9: A fi shan ruwa a kan abinci

Idan ba ka samu damar cin abinci ba kuma ka yi ƙoƙarin shan ruwa, kamar abin sha da ba shi da sinadarin ƙara kuzari, za ka rasa muhimman abinci mai gina jiki da kuma kuzari.

Wannan ba ɗabi'a ba ce mai kyau kuma ba za ta ɗore ba. Ƙara ruwan da kake sha yana da muhimmanci idan ka kasance mutum da ke cin abinci sau biyu saboda ba ka koshi da farko ba.

Shan ruwa kofi ɗaya kafin cin abinci zai sanya ka ji ka koshi da wuri. Miya za ta taimaka idan kana son rage kiba.

Camfi na 10: Motsa jiki shi ne hanya mafi dacewa wajen rage kiba

Mosta jiki ba shi da muhimmanci wajen rage kiba - yanayin cin abinci shi ke da kashi 70-80 na yin haka.

Mosta jiki yana da alfanu da yawa, ciki har da rage sinadarin ƙara kuzari, sai dai motsa jiki akai akai na ƙara karfin jijiyoyi, wanda ke da alaƙa da zama da kiba mai lafiya ta tsawon lokaci.

People are also reading