Home Back

KIWON LAFIYA: Gwamnatin Jigawa za ta riƙa kula da masu fama da ciwon ƙoda kyauta a faɗin jihar

premiumtimesng.com 3 days ago
Kotu ta daure mutumin da aka kama yana duldila ruwan sabulu a cikin ruwan da ake kara wa mara lafiya a asibiti
Hospital IV Drip in the patient room.

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta fara shirye-shiryen kula da masu fama da ciwon ƙoda kyauta a faɗin jihar.

A ƙarƙashin shirin, za a kafa sashen kula da masu ciwon ƙoda, ta hanyar yi masu gashin jiki, wato ‘dialysis’ a manyan asibitocin jihar guda biyar.

Kwamishinan Kula da Lafiya na Jihar Jigawa, Abdullahi Kainuwa ne ya bayyana haka ga manema labarai, bayan kammala taron Majalisar Zartaswa ta Jiha.

Ya ce Gwamnatin Jigawa ta amince a bayar da kwangilar aikin kafa cibiyoyin kula da masu fama da ciwon ƙoda da manyan asibitocin jihar da ke Dutse da Ringim, yayin da a yanzu haka aikin kafa na’urorin gashin jikin masu fama da cutar ƙoda ya kankama a manyan asibitocin Haɗejia, Kazaure da Gumel.

Kainuwa ya wannan hoɓɓasa na daga cikin Ajandoji 12 na Gwamna Umar Namadi, waɗanda suka haɗa har da kula da lafiya ga ɗaukacin al’ummar jihar Jigawa, babba ko yaro, talakawa da masu wadata.

“Gwamna Namadi ya ƙudiri ɗaukar nauyin tabbatar da cewa babu wani ɗan Jihar Jigawa da zai rasa ran sa saboda kasa biyan kuɗin magani a asibiti.”

Ya ƙara da cewa an kuma amince a kashe Naira biliyan 1.5 domin yin gyare-gyare a ƙananan asibitoci da cibiyoyin kula da marasa lafiya har guda 32 a mazaɓu 30 cikin Jihar Jigawa.

People are also reading