Home Back

An Bayar Da Belin DCP Abba Kyari

leadership.ng 2024/10/4
An Bayar Da Belin DCP Abba Kyari

An Bayar da belin mataimakin kwamishinan ƴansandan da aka dakatar, Abba Kyari, daga kurkukun Kuje da ke babban birnin tarayya bayan ya shafe watanni 27 a tsare.

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa NDLEA ce ta kama Abba Kyari a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 bisa zarginsa da haɗa baki da wata kungiyar safar ƙwaya ta kasa da kasa.

A ranar 7 ga Maris, 2022 ne aka gurfanar da shi gaban ƙuliya, tare da ƴansanda huɗu na rundunar leƙen asiri—Sunday Ubia da Bawa James da Simon Agirigba da kuma John Nuhu.

Duk da cewa an ƙi bayar da belinsa lokuta da dama, alƙalin babban kotun tarayya Emeka Nwite ya bayar da belin Abba Kyari a ranar 22 ga watan Mayu domin ba shi damar yin jana’izar mahaifiyarsa, Yachilla Kyari, wadda ta rasu a ranar 5 ga watan Mayu.

Bayan cika sharuɗɗan belin, an sake shi a jiya Juma’a, kamar yadda Adamu Duza, mai magana da yawun hukumar gyaran hali na Najeriya reshen babban birnin tarayya, ya tabbatar.

Abba Kyari

Kotun ta sanya ranar 31 ga watan Mayu, 2024, domin sauraren ƙarar da Kyari ya gabatar na neman beli dangane da tuhumar da ake masa na safarar miyagun kwayoyi. Bugu da kari, an gurfanar da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Chibunna Umeibe da Emeka Ezenwanne, wadanda aka kama a filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke Enugu a kan lamarin.

People are also reading