Home Back

RUƊANIN SARAUTAR KANO: Mataimakin Gwamna ya bai wa Ribadu haƙuri kan zargin tsoma hannu a dambarwar sarauta

premiumtimesng.com 2024/7/2
Hanyoyin Kawo Ƙarshen Matsalar  Tsaro a Najeriya – Nuhu Ribadu

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdulsalam ya nemi afuwar Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, bayan ya zarge shi da tsoma hannu da baki a dambarwar neman maida tuɓaɓɓen sarki Aminu Ado kan mulki.

Yanzu kuma Mataimakin Gwamna ya ce bayanan da ke gaban sa sun tabbatar cewa babu hannun Ribadu a cikin dambarwa, kuma ya ba shi haƙuri.

A ranar Asabar ce dai Gwamnatin Kano ta bakin Mataimakin Gwamna, ta zargi Ribadu da hannu wajen yunƙurin maida Aminu kan mulki da ƙarfin tsiya

A wani bidiyon da aka nuno shi ya na jawabi, Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam ya ce Nuhu Ribadu ne ke ƙoƙarin ƙaƙaba tsohon sarki kan mulki.

An tura sojoji tsaron Aminu Ado, bayan umarnin kama shi da Gwamnan Kano ya bayar

Rahotanni sun tabbatar da ƙarin jami’an tsaro na sojoji a fadar Nasarawa inda Aminu Ado ya kama.

Hakan na zuwa ne bayan umarnin kama tsohon sarkin da Gwamna Abba Kabir ya bayar a safiyar ranar Asabar.

Ƙarin sojoji ga Aminu ya zo yayin da Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam ya zargi Mashawarcin Musamman kan Tsaro na Shugaban Ƙasa, Nuhu Ribadu da ƙoƙarin yin amfani da ƙarfin jami’an tsaro don su maida Aminu kan mulki.

A ranar Asabar ce Ribadu ya ce ba da ɗaurin gindin sa aka maida tuɓaɓɓen sarki Kano ba.

Ofishin Mashawarcin Musamman na Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu ya ƙaryata zargin cewa shi ya bada jirage biyu domin maida tuɓaɓɓen sarki Kano, Aminu Ado zuwa Kano da daren Asabar.

Kakakin Ofishin NSA Zakari Mijinyawa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa zargin wanda Mataimakin Gwamnan Kano ya yi ba gaskiya ba ne. “Ribadu bai bada jirage a maida Aminu Ado Kano ba.

Ya yi kira ga ‘yan siyasa su iya bakin su, kada su kawo tarnaƙi ga zaman lafiyar Kano.

Wannan martani na zuwa ne daidai lokacin da gamayyar rundunar tsaro a Jihar Kano ta yi sanarwar cewa za su bi umarnin da Babbar Kotun Tarayya ta bayar kan rushe masarautu.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, Mohammed Gumel me ya bayyana wa manema labarai haka, a lokacin da ya ke tare da shugabannin sojoji, SSS, NSCDC, Hukumar Shige da Fice, Kwastan da sauran su.

Tuni dai Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi zaman fada, kuma ya koma cikin gida.

Cincirindon jama’a magoya bayan Sarki Sanusi sun yi dafifi a fadar sarki domin nuna goyon baya gare shi.

A ɗaya ɓangaren kuma Aminu Ado ya kafa fada a Gidan Nassarawa, gidan da ake binne gawarwakin wasu sarakunan Kano.

Shi ma Aminu ya amshi gaisuwa, kuma gamayyar shugabannin hukumomin tsaro na Kanoain kai masa ziyara, bayan sanarwar da suka yi wa manema labarai.

People are also reading