Home Back

Juyin Mulki: Shekaru 48 Da Kisan Janar Murtala Ramat Muhammad

leadership.ng 2024/5/6
Juyin Mulki: Shekaru 48 Da Kisan Janar Murtala Ramat Muhammad 

A rana 13 ga watan Fabrairun 1976, a ka kashe Shugaba mulkin Soja Na Tarayya Najeriya General Murtala Ramat Muhammad a Wani yunkurin juyin mulki da baiyi nasara ba.

An kuma kashe direbansa Da Gwamnan Mulkin Soja Na jihar kwara Kanal Ibrahim Taiwo.

Yunkurin juyin mulkin Nijeriya a shekarar 1976 wani yunkuri ne na juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijeriya ranar 13 ga Fabrairun 1976 a lokacin da wani bangare na hafsoshin Sojin kasar karkashin jagorancin Laftanar Kanar Bukar Suwa Dimka suka yi yunkurin kifar da gwamnatin Janar Murtala Mohammad. (wanda ya karbi mulki a juyin mulkin 1975 ).

An kashe Janar Murtala Muhammad a Legas tare da mataimakinsa Laftanar Akintunde Akinsehinwa a lokacin da wasu sojoji karkashin Dimka suka yi wa motarsa ​​kwanton bauna a Ikoyi kan hanyar zuwa Barrack Dodan.

A cikin shirye-shiryen Rediyo Da Aka watsa ga al’ummar kasar, Dimka ya ambaci cin hanci da rashawa, yanke hukunci, kamawa da tsarewa ba tare da shari’a ba, da rauni daga bangaren Gwamnatin Murtala da rashin iya gudanar da mulki a matsayin dalilan kifar da gwamnati.

Sojojin gwamnati Masu Biyayya Ga Gwamnati sun murkushe yunkurin juyin mulkin bayan sa’o’i da dama.

Bayan farautar makwanni uku, ana Neman Dimka Daga Bisani an kama Dimka a kusa da Abakaliki a kudu maso gabashin Najeriya a ranar 6 ga Maris 1976.

Laftanar Janar Olusegun Obasanjo ne ya gaji Janar Murtala Muhammad a matsayin shugaban kasa.

A lokacin da mulkin Obasanjo tare da makaranban shi a Gwamnati, da suka hada da shehu Musa Yar’adua da TY Danjuma da IBB da Domkat Bali sun yi kokarin ganin sun aiwatar da ayyukuna da Murtala ya kudurta gudanarwa a Najeriya.

Saboda kimar Janar Murtala Muhammad ne a Najeriya, aka saka hotonsa cikin kakin Soji a kudin kasar Naira Ashirin.

People are also reading