Home Back

Liverpool da Arsenal da Chelsea da West Ham na rububin ɗan bayan Bologna, Man Utd ta haƙura da Araujo

bbc.com 2024/10/5
Riccardo Calafiori

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool, da Arsenal, da Chelsea da kuma West Ham kowacce na son matashin ɗan bayan Italiya Riccardo Calafiori mai shekara 22, to amma fa dole duk wadda za ta saye shi ta biya abin da ya zarta fam miliyan 40 kafin ta raba shi da ƙungiyarsa Bologna. (Express).

Har yanzu wasu daga cikin darektocin Barcelona ba su gamsu ba a kan amfanin sayen tauraron ɗan wasan gaba na gefe na Sifaniya a gasar Euro 2024 fa Nico Williams, mai shekara 21, daga Athletic Bilbao ba (Sport - in Spanish).

Chelsea ta yi wa Brighton yankan baya, bayan da ta saye ɗan wasan tsakiya Kiernan Dewsbury-Hall, mai shekara, daga Leicester, bayan da tuni ɗan wasan mai shekara 25 ya riga ya yi gwajin lafiyarsa a Brighton ɗin kuma sun cimma yarjejeniya a kan farashinsa. (Telegraph )

Leicester na dab da cimma yarjejeniyar sayen matashin ɗan wasan tsakiya na Chelsea Michael Golding mai shekara 18. (The Athletic).

Newcastle na ƙoƙarin cimma yarjejeniyar sayen mai tsaron ragar Nottingham Forest da Girka Odysseas Vlachodimos, a matsayin wani ɓangare na musaya da matashin ɗan wasan tsakiya na Scotland Elliot Anderson mai shekara 21, zuwa Nottingham Forest. (Daily Mail).

Wataƙila Manchester United ta haƙura da maganar sayen ɗan bayan Barcelona Ronald Araujo, duk da sha'awarsa ɗan Uruguay ɗin da ta daɗe tana yi. (Football Transfers).

Kociyan Newcastle Eddie Howe, ya fito ƙarara ya gaya wa shugabannin ƙungiyar da kada su sayar da ɗan wasansa na gaba Alexander Isak, na Sweden a bazaran nan, yayin da Chelsea ke matuƙar sonshi. (Fabrizio Romano daga Teamtalk).

Tottenham na shirin tsawaita zaman ɗan gabanta na Koriya ta Kudu Son Heung-min har shekara ta 2026. (Football Insider)

People are also reading