Home Back

Ma’aikata Sun Nemi Gwamnoni Su Zaftare Albashin Su Don Su Iya Biyan Mafi Karancin Albashi

leadership.ng 2024/7/1
Ƙungiyar Ƙwadago Ta NLC Na Zanga-zanga Kan Ƙarin Ƙudin Wutar Lantarki A Nijeriya

Ma’aikatan gwamnati a Nijeriya sun bukaci gwamnonin jihohi da su rage yawan albashi da alawus-alawus da na wadanda suka nada mukamai domin samun damar biyan sabon mafi karancin albashi na N62,000 da gwamnatin tarayya za ta gabatar.

Ma’aikatan da suka zanta da manema labarai a jiya, sun soki gwamnonin kan cewa ba za su iya biyan sabon albashin ba.

Ma’aikatan sun ce za su kai karar gwamnoni idan sun ki aiwatar da sabon mafi karancin albashi idan gwamnatin tarayya ta amince da shi.

Wannan shi ne matsayar da kungiyar kwadago a Nijeriya ta bayyana kan matakin gwamnonin jihohi kan sabon mafi karancin albashi a matsayin rashin tunani da mugunta da son kai.

Kungiyar Gwamnonin Nijeriya, a ranar Juma’a, ta bayyana cewa gwamnatocin jihohi ba za su iya biyan Naira 60,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ba, kuma wasu jihohi za su koma karbar rance don biyan ma’aikata.

People are also reading