Badaƙalar Kuɗin Kwangila: ICPC Ta Cika Hannu da Daraktar TETFund
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta tsare Gloria Olotu, daraktar kudi da asusu ta hukumar tallafawa manyan makarantu (TETFund).
Wannan kuwa ya biyo bayan wani rahoto da jaridar Premium Times ta fitar a kwanan baya kan zargin an tafka badaƙalar N3.8bn a kwangilar da TETFund ta bayar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan jami'ai a hukumar ICPC sun bayyana cewa a ranar Alhamis sun gayyaci Mrs Oluto da Kolapo Okunola (daraktan sashen ICT na hukumar) da wani Joseph Odo domin amsa tambayoyi.
Sai dai hukumar ta sallami Okunlola da Odo ne kawai da cewar za su koma ofishin Hukumar ranar Juma'a yayin da ta tsare Mrs Oluto.
Rahoton da jaridar Premium Times ta fitar na yau Juma'a ya nuna cewa daraktar ta TETFund ta gaza cika sharuddan beli da aka dora mata.
Majiyar ICPC ta shaidawa jaridar cewa sun ayyana sunan Mrs Oluto a matsayin daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu a badaƙalar.
Mai magana da yawun hukumar da ke yaki da rashawar ta ICPC, Ademola Bakare ya tabbatar da wannan ci gaban a ranar safiyar Juma'a.
A ranar Litinin ne aka ruwaito cewa an tafka badaƙalar kudi da ta kai N3,812,500 a kwangilar da TETFund ta ba Makarantar Fides Et Ratio.
Kamar yadda ya sabawa dokar kasa, TETFund ta biya dan kwangilar N2.9bn a biya hudu, wanda tun asali ba a bi ka'ida wajen bayar da kwangilar ba.
An ce babu wata takarda ko hujja da ta nuna hukumar ta fitar da bayanan bayar da kwangilar kamar yadda dokar ba da kwangila ta tanadar.
A wani labarin kuma, makarantar Amurka da ke Abuja ta tuntubi hukumar EFCC kan batun kudin makarantar 'ya'yan Yahaya Bello, tsohon gwamnan jihar Kogi.
Makarantar AISA ta nemi ta mayarwa hukumar EFCC $760,910 da Ali Bello ya tura mata na kudin makarantar 'ya'yan Yahaya Bello bayan ta cike kudaden sabis.
Asali: Legit.ng