Home Back

Ba zan zauna a ofishina ba, yayin da ake faɗan Daba a birnin Kano – Kwamishinan Ƴan Sanda CP Dogo

dalafmkano.com 6 days ago

Sabon kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Salman Garba Dogo, ya ce ba zai ci gaba da zama a cikin ofishin sa ba, yayin da faɗan Daba, ke ƙara ta’azzara a cikin ƙwaryar birnin jihar.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, bayan wani rangadi da ya gudanar yau a cikin wasu daga cikin yankuna da ake fama da faɗan Daba a jihar.

“Daga cikin unguwannin da kwamishinan ƴan sandan ya yi ganawar da su akwai Dala, da Gwale, da kuma yankin Ɗorayi, da Ja’en, da kuma unguwar Sharaɗa, da sauransu, “in ji SP Kiyawa”.

Har ila yau, Kiyawa, ya ci gaba da cewa, CP Dogo, yayin ziyarar unguwannin ya kuma gana da wasu daga cikin shugabannin al’umma da ke yankunan, tare da ganewa idanun sa, domin lalubo hanyoyin magance harkokin faɗan Daba a sassan jihar Kano.

Dala FM Kano ta rawaito cewa rundunar ƴan sandan ta kuma ce, yanzu haka waɗanda aka kama da zargin Laifukan faɗan Daba a baya-bayan nan, musamman ma a unguwar Dala, da Ɗorayi, da Ja’en, har aka rasa rayuka, ana ci gaba da bincike domin ɗaukar mataki.

Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Salman Dogo, ya kuma ja hankalin al’umma da su ci gaba da bai wa rundunar haɗin kai musamman kan wani baƙon al’amari da suka gani ta waɗannan lambobi 08032419775, ko 08123821575, ko kuma 09029292926, domin bada agajin gaggawa.

People are also reading