Home Back

Yadda Na Ga Mata Suna Taimakon Iyaye Da Sana’a Ya Ja Hankalina Sosai —Khadija Sambo

leadership.ng 2024/6/30
Yadda Na Ga Mata Suna Taimakon Iyaye Da Sana’a Ya Ja Hankalina Sosai —Khadija Sambo

Khadija Sambo wata matashiya ce, wacce kasuwanci yake ba ta sha’awa musamman idan ta ga mata ‘yan uwanta suna yi suna taimaka wa kansu da iyayensu. Ta shawarce sauran ‘yan uwanta mata da su dage su yi karatu sannan kuma su kama sana’a domin dogaro da kai, kamar dai yadda za ku ji a cikin wannan tattaunawar da suka yi da BILKISU TIJJANI KASSIM.

Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki?
Sunana Khadija Sambo Lawan ni haifaffiyar Hadejia ce na taso a Garin Hadejia na yi karatuna a Garin Hadejia.

Shin ke matar aure ce?
A’a bani da aure muna dai sa rai in sha Allahu, kuma ni ‘yar kasuwa ce

Wanne irin kasuwanci kike yi?
Eh ina saida abubuwa da dama

Me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwanci?
Abin yana bani sha’awa idan na ga mata ‘yan uwana suna kasuwanci, sannan kuma suna taimaka wa kansu da iyayensu shi ne ya ja hankalina

Mene ne matakin karatunki?
Yanzu ajina biyu a jami’a

Wanne irin matsaloli kike fuskanta cikin wannan kasuwanci naki?
Matsalolin dai su ne akwai lokacin da aka turo min kaya a waya zan sara, sai bayan na sa an kawo min sai na ga ba kamar wanda na gani a waya ba.

Zuwa yanzu wanne irin nasarori kika cimma?
Gaskiya na cimma nasarori da dama na taimaka wa kannena wajen karatuna taimaka wa iyaye da ‘yan uwa da sauran mutane wannan ma nasara ce babba.

Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?
Abin da ya fi faranta min rai shi ne abubuwan da suka fi karfina a da yanzu na fi karfinsu a dalilin sana’ata

Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?
Ta kafofin sadarwar zamani, kamar WhatsApp, Facebook, Insgram, da dai sauransu.

Da me kike so mutane su rika tunawa da ke?
Ina so mutane su rika tunawa da ni a kan Jajircewata a sana’ata

Wacce irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?
Idan aka ce Allah ya yi wa rayuwata albarka, saboda wannan addu’ ar ta hada da komai ina jin dadi sosai

Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwa?
Gaskiya Ina samun goyan baya sosai suna karfafa min gwiwa akan karatuna da kasuwancina sosai, babu abin da zan ce musu sai addu’a da fatan alkhairi

Kawaye fa?
Ba ni da kawaye gaskiya

Me kika fiso a cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Kayan sawa na fi son atamfa kayan kwalliya hoda

A karshe wanne irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
Ina ba wa ‘yan uwana mata shawara akan mu yi karatu sannan mu koyi sana’a koda a ce mun kammala karatu babu aikin yi za mu iya rike kanmu da sana’armu mu taimaki kanmu da al’umma baki daya.

People are also reading