Home Back

Hajjin Bana: NAHCON Ta Ba Jihohi Wa’adin Mika Sunaye Maniyyata

leadership.ng 2024/5/7
NAHCON

Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya (NAHCON) ta bukaci hukumomi da rassan jihohi da ke kula da jin dadin alhazai da su gudanar da aikin tura jerin sunayen maniyyata a shafinta kafin karshen wannan makon.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa dauke da sanya hannun mataimakin daraktan sashin yada labarai na hukumar, Mousa Ubandawaki, da ya rabar wa ‘yan jarida a Abuja.

A cewar Ubandawaki, jerin rukunin sunayen mahajjatan na daga cikin bin matakai da ka’idojin rukuni-rukunin Tafweej na aikin hajjin 2024.

Ya ce kuma hakan zai saukaka wajen yin izinin shiga Saudiyya cikin sauki ta hanyar manhajar e-track.
“Jerin rukuni-rukuni ko gungu-gungun na da manufar saukaka hidimar samar da bizan Sadiyya ne. Kuma na daga cikin bin ka’idar da ya zama dole na rukuni-rukunin Tafweej na zirga-zirgan aikin hajjin 2024.

“Hukumomi a kasar Saudiyya sun bullo da wasu sabbin matakai daga cikin akwai cewa dole ne a yi rukuni-rukuni/gungu-gungun maniyyata 45 a kowani rukuni.

“Daga yanzu za a yi wa alhazai biza ne kawai ta hanyar rukunin mutum 45.”
Hukumar ta shawarci wadanda suke son kasancewa a tare da su tuntubi hukumar jin dadin alhazai na jihohinsu domin ganin an hadasu a jerin rukuni guda.

“Wadannan rukuni-rukunin na mutum 45 tare za su gudanar da dukkanin ayyukan aikin hajjinsu, tun daga tashi daga nan gida Nijeriya, masaukai da zirga-zirgansu a Makka da Madina, ayyukan Masha’ir da kuma dawowarsu nan gida Nijeriya.”

People are also reading