Home Back

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/06/2024

bbc.com 2024/7/5

Rahoto kai-tsaye

Yau za a fara jigilar alhazan Najeriya zuwa gida

Asalin hoton, NAHCON

..
Bayanan hoto, Alhazan Najeriya fiye da 50,000 ne suka sauke farali a wannan shekara

Nan gaba a yau ne Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON), za ta fara jigilar alhazan ƙasar daga Saudiyya zuwa Najeriya bayan kammala aikin Hajjin bana.

Hukumar ta Nahcon, za ta fara jigilar ne da alhazan Jihohin Kebbi da Nasarawa da kuma birnin tarayya Abuja, waɗanda dama su ne suka fara zuwa ƙasar mai tsarki.

Wakilin BBC da ya ziyarci wurin da ake aikin tantance kayan alhazan jihar Kebbi ya ce ya ga yadda ake auna jakankunan alhazan a mataki na ƙarshe kafin ɗaukar su zuwa filin jirgin saman Jedda domin su shiga jirgi zuwa Najeriya.

Alhazzan da suka fito daga ƙananan hukumomin Arewa da Jega dakuma Kalgo ne za su fara tashi a Jirgin farko.

Cikin sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan jihar, Ahmed Idris ya fitar, ya ambato shugaban hukumar Alhazan jihar, Alhaji Faruku Aliyu-Enabo na cewa alhazan da suka fara zuwa a jirgin farko, su ne za su fara tashi a jirgin farko da zai tashi daga Saudiyya.

"Haka kuma alhazan da suka je a jirgin ƙarshe, za su zama a jirgin ƙarshe da zai kammala jigilar mahajjatanmu", in ji Alhaji Faruku Aliyu-Enabo.

Kimanin jirage 121 ne suka yi jigilar mahajjatan Najeriya fiye da 50,000, a wannan shekara, kamar yadda hukumar ta Nahcon ta bayyana.

People are also reading