Home Back

Ƙarin kuɗin ruwa zuwa kashi 30 bisa 100 da CBN ya na hana masana’antu ɗaukar ma’aikata

premiumtimesng.com 2024/7/15
BA RUWAN ARZIKI DA MUGUN GASHI: Korona ba ta hana su Ɗangote ƙara kuɗancewa cikin 2021 ba
Aliko-Dangote

Shugaban Rukunin Kamfanoni da Masana’antun Dangote Group, Aliko Ɗangote, ya soki ƙarin kuɗin ruwa da Babban Bankin Najeriya, CBN ya yi zuwa kusan kashi 30 bisa 100.

Ya yi wannan sukar a lokacin da yake jawabi yayin buɗe Taron Kwana Uku da Ƙungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya (MAN) ta shirya, a Babban Ɗakin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa, ranar Talata, a Abuja.

Aliko, wanda shi ne mafi ƙasaitaccen attajiri a Afrika, ya ce a wannan hali na kuɗin ruwa da banki ke ɗora wa masu ramcen kuɗi har kashi 30 bisa 100, to zai yi wahala masana’antu su riƙa ɗaukar ma’aikata, kuma babu yadda za a yi tattalin arzikin ƙasa ya bunƙasa, ballantana har a ce a yi gagayya da sosai da sosai.

Kwanan baya ne dai CBN ya maida kuɗin ruwa zuwa kashi 26.25 daga 24.74.

A cikin watan Fabrairu ne dai aka ƙara kuɗin ruwan zuwa 22.75 daga 18.75. Daga nan kuma cikin watan Maris aka ƙara kuɗin ruwa suka koma kashi 24.74% bisa 100%.

Yanzu kuma an ƙara daga kashi 24.75 zuwa kashi 26.65%.

Ko a kwanan nan sai da Bankin Duniya ya gargaɗi CBN cewa ba zai iya daƙile tsadar kaya da tashin farashi ta hanyar ƙara kuɗin ruwa ba. Ya ce yin hakan ka iya haifar da barazana ga tattalin arzikin Najeriya.

Shi kuwa Ɗangote kira ya yi a fito da tsare-tsaren da za su kare masana’antun cikin gida, tare da yin kira ga gwamnatin tarayya ta kare hada-hadar cikin gida, musamman masana’antu da masu masana’antun ta hanyar sama masu damar yin hada-hada ba tare da tsawwala masu ba.

“Amma maganar gaskiya babu wata masana’anta ko kamfanin da zai iya samar wa mutane aiki yayin da banki zai ɗora ke ɗora masa kashi 30% bisa 100% na kuɗin ruwa. Kuma tattalin arzikin ƙasar nan ba zai iya yin gaba ba.” Inji Ɗangote.

People are also reading