Home Back

Dangote ya kaddamar tallafin buhunan shinkafa a Kano

dailynews24.ng 2024/5/2

Gidauniyar Aliko Dangote, ta bayar da gudunmawar buhunan shinkafa mai nauyin Kilogram 10, don a raba wa marasa karfi fiye da mutane miliyan daya wadanda kimar kudinsu kai naira biliyan 15 a fadin kasarnan.

Da yake kaddamar da rabon kayan abincin a jahar Kano, Hamshakin Attajirin Afrikan, kuma shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce an gudanar da aikin rabon kayan lokaci guda a Kano da Lagos.

A cewar Dangote, wannan kudirin an shi ne domin tallafa wa marasa karfi dake cikin al’umma, bisa matsin tattalin arziki da ya jefa talakawa cikin kuncin rayuwa.

Ya kara da cewa babban burin gidauniyar Dangote shi ne, fadada aiyukanta a dukkanin jahohin Nigeria 36, ciki harda birnin tarayya Abuja don tabbatar da cewa al’ummar Nigeria sun amfana da shirin tallafin musamman a wannan laokaci na Azumin Ramadana.

A jawabinsa gwamnan jahar Kano, Engr, Abba Kabir Yusuf , ya yaba da irin aiukan jinkan da Aliko Dangote, yake yi a fadin Nigeria dama sauran kasashen Afrika.

Gwamnan ya bukaci yan kwamitin dake kula da rabon kayayyakin da su tabbatar da an ba wa wadanda suka cancanta.

Gwamma Abba Kabir , ya yi kira ga sauran ma su hannu da shuni da suke cikin al’umma da su yi koyi da gidauniyar Dangote wajen tallafa wa al’umma.

People are also reading