Home Back

Siyasa Ta Rikiɗe: Gwamna Ya Takali Mai Gidansa, Ya Kori Shugaban Majalisar Sarakuna

legit.ng 2024/7/3
  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya sallami shugaban Majalisar sarakuna a jihar ana tsaka da rikicin siyasa
  • Fubara ya ce kori Chidi Awuse ne tare da maye gurbinsa da Eze Chike Worlu Wodo saboda rashin iya shugabanci
  • Awuse ya kasance na hannun daman Ministan Abuja, Nyesom Wike wanda ba su ga maciji da Gwamna Fubara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya sallami shugaban Majalisar sarakunan gargajiya a jihar.

Fubara ya kori Mai Martaba Chidi Awuse wanda ya kasance na hannun Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Gwamnan ya maye gurbin Awuse da mai sarautar Apara, Eze Chike Worlu Wodo, Daily Trust ra tattaro.

Har ila yau, gwamnan ya ce ya sauya Awuse saboda rashin shugabanci mai inganci a matsayin mai jagorantar Majalisar sarakunan..

Sabon shugaban Majalisar, Wodo ya kasance mai sarautar Apara da ke karamar hukumar Obio/Akpor a jihar, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fubara ya ce Majalisar sarakunan sun buga kalanda na 2024 inda suka ci mutuncin gwamnanin jihar.

Gwamnan ya ce Majalisar ya ki saka hotunan gwamnan jihar da kuma mataimakinsa wanda hakan kaskanci ne.

Ya ce hakan ya tabbatar da cewa Majalisar ba za ta iya gudanar da shugabanci yadda ya kamata ba.

Fubara ya umarci binciken tsofaffin ciyamomi 23

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya umarci binciken tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi a jihar Rivers.

Fubara ya dauki matakin ne yayin da ake zargin tsofaffin ciyamomin da almundahana lokacin da suke mulki.

Hakan ya biyo bayan karewar wa'adin ciyamomin 23 a ranar 17 ga watan Yunin 2024 bayan shafe shekaru kan mulki.

Asali: Legit.ng

People are also reading