Home Back

NOMA DA TATTALIN ARZIKI: Gwamnatin Jigawa za ta raba wa masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i lamunin Naira biliyan 6

premiumtimesng.com 2 days ago
NOMA DA TATTALIN ARZIKI: Gwamnatin Jigawa za ta raba wa masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i lamunin Naira biliyan 6

Gwamnatin Jigawa ta bayyana cewa za ta raba wa manoma da masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i bashin Naira biliyan 6, a ƙarƙashin Bankin Bunƙasa Masana’antu (BoI).

Da yake sa hannu a daftarin yarjejeniyar da Gwamnatin jihar ta ƙulla da BoI, a Dutse babban birnin jihar, a Gidan Gwamnati, Gwamna Umar Namadi ya ce wannan lamuni an bijiro da shi ne domin tallafawa ga musamman masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i, musamman a ɓangaren da ya fi shafar harkokin noma.

Gwamna Namadi ya ce, “A yau wannan shiri wani somin-taɓin ci gaba ne aka fara samu a ƙoƙarin da muke yi na rage raɗaɗin talauci da kuma himmar samar wa ɗimbin jama’a aikin yi da kuma bunƙasa tattalin arziki.”

Namadi ya ce ƙara zaburar da mutane da taimaka masu a fannin sana’o’in da suka zaɓar wa kan su da kansu, tsari ne da muka bijiro da shi domin gaggauta samar da ci gaba da kuma bunƙasa jiha. “To kuma Bankin BoI abokin haɗin-guiwa ne domin cimma samun nasarar wannan kyakkyawan ƙudiri.”

“Sa hannu kan wannan yarjejeniya da BoI domin raba wa masu ƙanana, matsakaita da manyan sana’o’i wannan bashi muhimmin abu ne sosai a ƙoƙarin samar da cigaba da muke yi a Jihar Jigawa.

“Muna murna da samun Reshen Bankin BoI a jihar mu a yanzu, kuma duk wasu cibiyoyin gwamnati masu haƙƙi an jawo su domin ilmantarwa da wayar da kai ga masu sha’awar samun wannan dama ta karɓar lamuni daga bankin.”

“Gwamnati za ta tabbatar da cewa an cika dukkan sharuɗɗan da bankin ya gindaya, kamar yadda doka ta tanadar, domin a tabbatar jama’ar da suka cancanci karɓar lamunin ne kaɗai za su ci moriyar sa.”

Shi kuwa Babban Daraktan Ƙanana da Matsakaitan Sana’o’i na BoI, Shekarau Umar, ya bayyana cewa wannan bashi na Naira biliyan 6 da za a raba wa manoma da masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i a Jigawa, shi ne mafi yawa a dukkan sauran jihohin ƙasar nan.

“Mun shafe shekaru 13 kenan muna rubuto wasiƙu cewa BoI na so ya kafa reshe a Jihar Jigawa, amma ba a ba su goyon baya, sai a wannan gwamnatin. Mun samu amincewa a cikin watanni shida, Gwamna Umar Namadi ya cika mana burin mu, ya maida mafarkin mu ya zama gaskiya.”

People are also reading