Home Back

Malamin Musulunci Ya Kunyata ’Yan Siyasa a Zaman Makokin Tsohon Gwamna

legit.ng 2024/8/23
  • Malamin Musulunci, Sheikh Muhydeen Bello ya caccaki 'yan siyasa kan yawan gaba da suke yi a tsakaninsu
  • Malamin ya bayyana haka yayin bikin tunawa da marigayi tsohon gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi a birnin Ibadan
  • Shehin malamin ya bayyana 'yan siyasar Najeriya a matsayin marasa tsoron Allah da son abin duniya duk da dukiyarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Malamin addinin Musulunci ya gargadi 'yan siyasa kan amfani da lokacinsu wurin aikata ayyukan alheri.

Malamin mai suna Sheikh Muhydeen Bello ya ce wata rana za su zamo Allah sarki bayan barin ofisoshinsu.

Shehin malamin ya bayyana haka ne yayin bikin tunawa da tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi a Ibadan da ke jihar, cewar Punch.

Ya ce 'yan siyasar Najeriya ba su da godiyar Allah kan abin da ya hore musu inda ya ce mafi yawa ba su tsoron Allah.

"Yan siyasa ba su bukatar dukiya, amma ba su taba godewa Allah da abin da suke da shi, ba ku da tsoron Allah, kuna tare da Ajimobi amma kun yake shi."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Har yanzu wasu suna jin haushinsa duk da yana cikin kabari, kowa zai wuce kamar yadda Ajimobi ya bar duniya."
"Ba tare da hadin kai ba, ba za a iya ci gaba da ayyukan alheri na Ajimobi ba, yana da jama'a sosai da suka damu da shi."

- Muhydeen Bello

Malamin ya ce a matsayinsu na 'yan siyasa ya kamata su so junanku, Ajimobi ya rasu ya bar mutane a bayansa, ya kamata kowa ya bar abin da za a iya tunawa da shi a duniya.

Sheikh Bello ya bukace su da su kasance cikin zaman lumana da 'yan uwansu ba tare da gabar siyasa ba.

Malamin Musulunci ya magantu kan sarautar Kano

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen malamin Musulunci a Gombe, Sheikh Adamu Dokoro ya magantu kan rigimar sarautar Kano.

Malamin ya ba Abba Kabir da Sanusi II da Aminu Ado Bayero shawarwari kan gudanar da komai domin Allah a jihar.

Asali: Legit.ng

People are also reading