Home Back

Ganduje Na Nan a Matsayin Shugaban APC Na Kasa Bayan Hukuncin Kotu? Bayanai Sun Fito

legit.ng 2024/5/19
  • Jam'iyyar APC ta jaddada cews Dakta Abdullahi Umar Ganduje na nan daram a matsayinsa na shugaban jam'iyyar na ƙasa
  • Mai magana da yawun APC, Felix Morka, ya ce ba za su yi aiki da umarnin kotun farko ba, amma suna tare da hukuncin babbar kotun tarayya
  • Morka ya bayyana cewa a yanzu komai ya koma asalin yadda yake gabanin dakatar da Ganduje a gundumarsa da ke Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta ƙasa ta ce ba za ta yi amfani da umarnin babbar kotun Kano na farko ba wadda ta tabbatar da dakatar da Abdullahi Ganduje.

Mai magana da yawun APC na ƙasa, Felix Morka, ya jaddada cewa jam'iyyar ba za ta kalli umarnin kotun farko na dakatar da Ganduje daga matsayin shugaban APC.

Shugaban APC, Abdullahi Ganduje.
Ganduje zama daram a kujerar shugaban APC, in ji Felix Morka Hoto: OfficialAPCNig Asali: Twitter

Ya kuma nanata cewa har yanzun ba a kawo ma shugaban jam'iyya mai mulki takardar umarnin kotun ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Morka ta yi wannan furucin ne yayin da ya baƙunci wani shiri na gidan talabijin din Arise.

Maimakon haka, kakakin APC ya tabbatar da cewa suna goyon bayan hukuncin babbar kotun tarayya mai zama a Kano, wadda ta ɗage umarnin dakatar da Ganduje.

Kotu ta bada sabon umarni

Rikicin siyasar Kano ta ɗauki sabon salo bayan babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta tabbatar da Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar APC ranar Laraba.

Kotun dai ta ɗauki wannan matakin ne bayan tsohon gwamnan Kano ya shigar ƙarar neman a bi masa haƙƙinsa na saurarom ɓangarensa.

Da yake mayar da martani, Morka ya ce wannan shi ke abin da ya dace saboda duk wannan kace-nace da ake ta yi waɗanda suka dakatar da Ganduje ba ƴaƴan APC ba ne.

Kakakin APC ya ce:

"Bai kamata kotun farko ta ba da wannan umarni ba saboda wasu dalilai. Na farko waɗanda suka shigar da ƙarar ba mambobin APC ba ne ba su da hurumi."

Wanene sahihin shugaban APC?

Mai magana da yawun APC ya ƙara da cewa bayan hukuncin babbar kotun tarayya, a yanzu komai ya koma asalin yadda yake gabanin lamarin dakatarwan nan ya ɓullo.

"A halin yanzun mun koma asalin yadda muke gabanin dakatar da Ganduje, yana nan daram a matsayin shugaban jam'iyya mai mulki ta ƙasa."

Ganduje ya ƙara shiga matsala

A wani rahoton kuma masu zanga-zanga sun kutsa kai babbar hedkwatar APC da ke Abuja kan batun dakatar da shugaban jam'iyya na ƙasa, Abdullahi Ganduje.

Sun buƙaci a soke duk wani mataki da Dr. Ganduje ya ɗauka bayan dakatar da shi kuma sun aike da saƙo ga shugaban ƙasa Tinubu.

Asali: Legit.ng

People are also reading