Home Back

Ana Tsaka da Neman Gurbi a Kofin Duniya, Kocin Super Eagles, Finidi Ya Yi Murabus

legit.ng 2024/7/5

Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa kocin Super Eagles, Finidi George ya yi murabus daga mukaminsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An ruwaito cewa kocin kungiyar Super Eagles, Finidi George ya yi murabus daga mukaminsa.

Murabus din bai rasa nasa da rashin tabuka wani abu bayan karbar ragamar Super Eagles da Finidi ya yi.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da dan jarida a bangaren wasanni, Adepoju Tobi Samuel ya walllafa a shafin X.

"Majiyoyina sun tabbatar min cewa Finidi George ya yi murabus daga mukaminsa na kocin Super Eagles."

- Tobi Samuel

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani dan jarida a bangaren wasanni, Sulaiman Pooka Adebayo shi ma ya tabbatar da haka.

"Finidi George ya yi murabus bayan mayar da shi baya yayin da za a dauko koci daga kasar waje."

- Sulaiman Pooja

Super Eagles za ta dauko sabon koci

Hukumar kula da kwallon kafar Najeriya (NFF) ta yanke shawarar dauko hayar mai horar da 'yan wasa daga Turai domin jan ragamar tawagar Super Eagles.

An ce NFF za ta dauko wa Super Eagles hayar koci daga Turai biyo bayan shan kashin da tawagar ta yi a wasanni biyu jere, karkashin Finidi George.

Asali: Legit.ng

People are also reading