Home Back

"Girma Ya Fadi": An Cafke Basarake da Sabon Kansila Kan Zargin Satar Tiransifoma

legit.ng 6 days ago
  • Dubun wasu masu girma a cikin al'umma ta cika bayan cafke su da satar tiransifomar wutar lantarki a jihar Gombe
  • Rundunar ƴan sanda ta yi nasarar cafke kansila da kuma dagacin kauyensu kan zargin sats da kuma siyar da tiransifoma
  • Kansilan mai suna Abdullahi M Panda yana wakiltar Kumo ta Gabas ne a karamar hukumar Akko da ke jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Rundunar ƴan sanda a jihar Gombe ta cafke wani kansila kan zargin sace tiransifoma a jihar.

Ana zargin kansilan yankin Kumo ta Gabas a karamar hukumar Akko da ke Jihar mai suna Abdullahi M Panda da sata.

Ƴan sandan sun cafke shi ne tare da Jauron Majidadi, Muhammad Majidadi da wani mutum daya bayan sun siyar da tiransifomar wutar lantarkin.

Kakakin rundunar ’yan sanda a jihar, ASP Buhari Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sun cafke su ne bayan samun bayanan sirri.

Buhari Abdullahi ya ce bayan gudanar da bincike, an gano sun siyar da tiransfomar kan kudi N1.5m ga wani mai suna Bello Ardo Kumo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an karbo tiransifomar kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.

Sai dai kansilan a bangarensa ya ce sun yi magana da dagacin kauyen kan lamarin inda ya bukaci su kawo a rubuce.

Ya ce daga bisani sun kira mai saye ranar Juma’a inda ya ke kokarin daukar tiransifomar domin siyarwa ’yan sanda suka kama su.

Amma ya bukaci a kai su kotu domin a can ne zai shaidawa kotu abin da ya sani domin wanke kansa daga zargi.

An kawo sabon tsarin almajirai a Gombe

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin jihar Gombe ta amsa kiran da aka daɗe ana yi kan kawo gyara a harkar almajiranci a Najeriya.

Gwamnatin da dauki matakin samar da adadin almajirai a fadin jihar kan kokarin saka tsare-tsaren zamani a harkar almajiranci.

Asali: Legit.ng

People are also reading