Home Back

Ana Shirin Sallah, Darajar Naira Ta Yi Raga Raga a Kasuwa

legit.ng 2024/6/28
  • Darajar Naira ta faɗi kan Dalar Amurka a kasuwar musayar kuɗi ta gwamnati da ta ƴan canji a ranar Juma'a
  • Duk da cewa darajar Naira ta ƙaru a farkon mako, daga baya darajar ƙuɗin na Najeriya sun yi ƙasa kan Dalar Amurka
  • Tasirin faɗuwar darajar Naira dai zai shafi al’ummar Musulmi da ke fatan gudanar da bukukuwan Sallar Eid-el-Kabir a daidai lokacin da ake ƙara samun tsadar kayan abinci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - A ranar Juma’a, 14 ga watan Yuni, 2024, darajar Naira ta faɗi a kasuwar ƴan canji.

A cewar ƴan kasuwar canjin kuɗin waɗanda aka fi sani da ‘Bureau de Change (BDC)’, darajar Naira ta faɗi zuwa N1,485 kan kowacce dala.

Darajar Naira ta fadi a kasuwa
Darajar Naira ta fadi a kasuwar 'yan canji ana shirin yin Sallah Hoto: Jean Chung, Legit.ng Asali: UGC

Naira ta kasa samun daidaito

Ƴan kasuwar canjin kuɗin suna siyan Dala kan N1,460 sannan su sayar da ita a kan N1,485, wanda hakan ya haifar da ribar N25, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Faduwar ta nuna an samu raguwar N5 ko 0.34% daga farashin N1,480/$ da aka samu wata guda da ya gabata a ranar 10 ga watan Mayu.

Haka kuma a ranar Juma’a da ta gabata, darajar Naira ta ragu da kaso 0.44%, wato N6.48, zuwa N1,482.72 kan kowacce dala a kasuwar musayar kuɗi ta FMDQ da ke kula da kasuwancin musayar kuɗaɗen waje a Najeriya.

A cikin sa'o'in ciniki, Dala ta kai sama da Naira 1,490 da kuma farashi mafi ƙaranci na N1,390. A wannan farashin, bambanci tsakanin kasuwar gwamnati da ta ƴan canji shine N2.28.

Faduwar darajar Naira za ta shafi bikin Sallah

Sau da yawa faduwar darajar Naira a kan Dala na shafar farashin kayayyakin abinci a kasuwanni, wanda hakan ke rage ƙarfin sayen kayayyaki na ƴan Najeriya.

Sai dai, a wannan lokacin tasirin faɗuwar darajar Naira zai shafi al'ummar musulmai wajen siyan kayan abinci da raguna domin bukukuwan Sallah.

Darajar Naira ta ƙaru

A wani labarin kuma, kun ji cewa darajar Naira ta ƙara tashi a kasuwar ƴan hada-hadar kuɗi ta bayan fage, inda ta dawo N1,500 kan kowace Dala ranar Talata, 28 ga watan Mayu.

Naira ta ƙasa farfaɗowa a jiya Talata daga N1,520 da aka yi musanyar kuɗin Najeriya kan kowace Dalar Amurka ɗaya a ranar Litinin, 27 ga watan Mayun 2024.

Asali: Legit.ng

People are also reading